Abinda ya sa NLNG hana sayar da gas ga ƙasashen waje

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai hukumar hada-hadar Gas ta Gwamnatin Tarayyar Nijeriya (NLNG) ta ba da odar hana fita da gas zuwa wasu ƙasashen sai dai a sayar da shi ga dilolin cikin gida. Abinda ya jawo ruguzowar farashin gas ɗin girki ga al’ummar ƙasar. 

Wannan umarni na NLNG ya zo ne a dai-dai lokacin da jama’a suke kokawa da yadda farashin gas ɗin ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar tun daga watanni biyar da suka wuce. 

Hukumar Rarraba gas ɗin ta Nijeriya ta bayyana cewa, ana sa ran nan gaba kaɗan za ta sauko da farashin gas ɗin ya sakko ya yi rugu-rugu.  Domin a cewar NLNG ɗin ba wani abu ya sa suka hana fitar da gas ɗin zuwa ƙasashen waje ba illa sai domin a dinga sayar wa da dilolinsa na cikin gida (Nijeriya), domin ya wadace su, su kuma su sayar da shi a farashi mai sauƙi.  

Kwamitin daraktocin  NLNG shi ya ba da sahalewarsa a ranar Litinin 13 ga watan Janairun, 2022. Inda ya bayyana cewa lallai sai dai  a sayar da gas ɗin ga ‘yan kasuwar cikin gida banda fitar da shi a sayar da shi a ƙasashen ƙetare.