Mafi yawan kuɗin tallafin Gwamnatin Tarayya sun salwance, cewar Gwamna Bala

Daga BAKURA K. MUHAMMAD A Bauchi

Mafi yawancin kuɗaɗe daga cikin nairori tiriliyan guda da biliyan ɗari biyar da Gwamnatin Tarayya ta keɓe domin tallafa wa ‘yan ƙasa marasa ƙarfi sun salwance cikin aljifan jami’an gwamnati da masu riƙon muƙaman siyasa da ke ƙarƙashin jagorancin gwamnatin APC ta Shugaba Muhammadu Buhari, a cewar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.

Gwamnan, ya kuma yi la’akari da cewar, shirin taimako na SIP wanda kututun sa ake shirin domin taimaka wa marasa ƙarfi su fice daga cikin ƙangin talauci, tare da inganta rayuwarsu, ana karkata su ne bisa rashawa da cin hanci domin cimma muradun wasu masu idanuwa da kwalli a jam’iyyar APC masu mulki.

Bala, ya yi wannan furuci ne a garin Misau a ranar Laraba da ta gabata yayin ƙaddamar da shirin tallafin kyautar kayayyakin sana’a da kuɗaɗen zuba jari wa marasa ƙarfi, inda ya lura da cewar, tuni ma wannan shiri na gwamnatin tarayya ya sha ƙasa sakamakon dabaibayar sa da tumasanci ya yi.

Ya ce, “gaskiya ne Gwamnatin Tarayya da muƙarraban ta tuni suke ta tutiyar samar da tallafi, amma muna ƙalubalantar su da cewar, akwai almundahana a cikin nasu shirin. Mu muna bayar da tallafi ne Lillahi Wa Rasuluhi ta yadda za ake fitar da masu ƙananan ƙarfi daga ƙangin talauci a zahirance.

Gwamnan ya bayyana cewar, shirin tallafin na gwamnatin jihar Bauchi ya yaɗu ko’ina cikin al’ummomin jiha daban-daban, waɗanda suka haɗa da masu sana’o’i daban-daban kamar tuyar ƙosai, kafina, teloli, magina, masu sana’ar ƙuli-ƙuli, waɗanda za a koma masu kamun kifi, ba a ba su kifin ba, ƙananan ‘yan kasuwa, da dai gomman makamantan su, a inda a cikin qaramar hukumar Misau kawai ake kashe zunzurutun kuɗaɗe Naira miliyan saba’in da biyar.

Bala, ya kuma yi la’akari da cewar, wannan shine karo na farko a matakin gwamnatin jiha a Bauchi da aka ƙaddamar da irin wannan shiri, yana mai cewar, “ba kuɗaɗe da aka kashewa su ne abin lura ba, domin idan aka duba ita gwamnatin tarayya tana kashe zunzurutun kuɗaɗe har Naira tiriliyan guda da Naira biliyan ɗari biyar, amma mafi yawancin waɗannan kuɗaɗe suna sulalewa ne cikin aljifan jami’an gwamnatin APC da ‘ya’yan siyasar ta mayaudara.”

A bisa wannan taɓargaza ne, gwamnan ya lura da cewar, tuni ma shirin tallafin na gwamnatin tarayya ya warwatse, domin kamar yadda ya ce a halin yanzu “babu wani mutum, hukuma, gwamnatin jiha ko na ƙananan hukumomi da ke yake samun wani tallafi daga cikin shirin, komai ya tsaya cik, kuma muna yin ƙananan maganganu domin a samu gyara, ba domin gatsali wa shugaban ƙasa ba.”

Ya shaida wa Shugaban Majalisar Amintattu ta jam’iyyar PDP (BoT), Sanata Walid Jibrin wanda a ranar ta Laraba ya ƙaddamar da makamancin shirin tallafin na jiha a ƙaramar hukumar Dambam, daya samu rakiyar sakataren majalisar amintattun – Sanata Adolpus Wabara cewar, “mu na matuƙar fahari da zuwan ku jihar Bauchi domin ganin yadda muke shimfida siyasar mu. Da masu gudanar da wannan shiri ba jajirtattu ba ne, da ba mu hallara a wannan waje ba, inda gaskiya da adalci suka yi katutu.”

Bala ya jaddada cewar, “a Bauchi ba mu da gefe ko ɓaraka, babu kace-nace, mutane masu biyayya ne wa hukumomi, da jam’iyya bisa adalci da ake yi masu. Jam’iyyar mu ta PDP a matakin ƙasa tana ƙarƙashin jagorancin fitaccen masani Walid Jibrin, ni kuma a matsayina na gwamna mai biyayya ne ga jam’iyya da jama’a.”

Gwamnan ya yi kuma tuni da cewar, garin Misau ne asalin mahaifiyar sa bisa la’akari wanda ya kafa garin Alkaleri inda aka haife ta, wata Alƙali Haruna daga garin Misau ya taso, don haka ni ma asalina garin Misau ne bisa dubi da asalin mahaifiya ta, yana mai jaddada cewar, “ina mai matuƙar girmama garin Misau, kuma idan ban yi wa garin Misau wani tagomashi ba, to nayi wa kai na.

“Dangane da haka, kuma bisa al’ada ta na sakayya wa al’ummar garin Misau, zan gina hanya sabuwa fil daga garin Misau zuwa Akuyam, mahaifar shugaban jihar Bauchi na jam’iyyar PDP, Alhaji Hamza Ƙoshe Akuyam ta haɗa da Hardawa zuwa Zadawa.

“Abin takaici ne a ce dukkan hanyoyin da suka ratsa shiyyar tsakiyar jihar Bauchi, hanyoyin gwamnatin tarayya ne. Wannan lamari babu adalci a ciki, ko hanyar da aka zayyana za a gina da za ta tashi daga Soro zuwa Miya, wani dan siyasa ya zamna akan kuɗaɗen aikin da ya zarce naira biliyan guda. Sun karɓe kuɗaɗen aikin hanyar, su nyi ƙememe a kai, a yanzu haka muna cikin kotu da su, ba kuma za mu bar masu waɗannan maƙudan kuɗaɗe ba.”

Gwamna Bala ya bai wa shugabannin ƙaramar hukuma ta Misau cewar, gwamnatin sa zata gina hanya daga Akuyam zuwa Hardawa zuwa Zadawa, kazalika da wacce ta taso daga Soro zuwa Miya, ya qara da faɗin “babu wani ɓangare a jihar Bauchi da za mu yi masa giɓi wajen samar da abubuwan more rayuwa.”