Jirgin ƙasa ya niƙe tirela da ƙananan ababen hawa a Kano

Daga WAKILINMU

Bayanai daga Jihar Kano sun nuna an samu aukuwar mummunan haɗari inda jirgin ƙasa ya niƙe tirelar ɗaukar siminti mallakar kamfanin Ɗangote da wani a-dai-daita-sahu.

Haɗarin ya auku ne ran Lahadi da misalin ƙarfe 11:30am a kan hanyar Obasanjo a Kano.

Bayanan shaidu sun ce an ga lokacin da tirelar ta nufo layin dogo a daidai lokacin da jirgin ke shirin wucewa.

Sun ce an yi ƙoƙarin jan hankalin direban motar don ankarar da shi ga jirgi nan tafe amma ina, bai hankalta ba.

An ce jirgin ya daki motar ne a lokacin da direban ya yi ƙoƙarin tsallake hanyar jirgin wanda ya haɗa da wani a-dai-daita-sahu da ke kusa.

Shaidun sun ƙara da cewa, faruwar haɗarin ke da wuya sai aka kwashi waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti, yayin da shi direban tirelar ko rauni bai ji ba.