Kasuwanci

USAID ta bada tallafi ga manoman rogo 100 a Kwara

USAID ta bada tallafi ga manoman rogo 100 a Kwara

Daga AMINA YUSUF ALI Kimanin ƙananan manoman rogo guda 100 ne dai 'yan asalin jihar Kwara suka samu tagomashin tallafi daga ƙungiyar tallafi ta Amurka (USAID) don bunƙasa harkar noma.  An zavo waɗannan manoman rogo ne daga ƙananan hukumomin jihar Kwara. Inda aka fara da ba su kayan aiki da kuma horaswa a fannin noman zamani domin ingantawa da bunƙasa sana'arsu.  Mashiryin shirin ba da tallafin jarin ga manoman rogon, Mista Banjo Famuyiwa, ya bayyana cewa, wannan shirin USAID a Nijeriya ce ta ɗauki nauyinsa tare da haɗin gwiwar AYOSIFAM da ma'aikatar faɗaɗa aikin noma da raya karkara ta jihar…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta buɗe kasuwar gwal a Kano

Gwamnatin Tarayya za ta buɗe kasuwar gwal a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin cewa, nan da watanni 10 masu zuwa za ta kammala gini sannan kuma ta buɗe kasuwar gwal ɗin da take ginawa a Jihar Kano.  Ministan tama da ƙarafa na tarayyar Nijeriya, Arc Olamilekan Adegbite, shi ya tabbatar da haka a yayin wata ziyarar rangadi da ya kai ga kasuwar da ake ginawa a halin yanzu a jihar Kano.  Waɗannan jawabai suna ƙunshe ne a cikin wata takarda da kakakin Ma'aikatar tama da ƙarafa, Idowu Jokpeyibo ya wallafa. A cikin jawabin, an bayyana cewa, Shugaba Buhari na Nijeriya ya yi alƙawarin cewa,…
Read More
Ƙarancin fetur: Gunagunin ’yan Nijeriya ya sa NNPC kwana rabon mai

Ƙarancin fetur: Gunagunin ’yan Nijeriya ya sa NNPC kwana rabon mai

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Talatar da ta gabata ne Kamfanin dillancin man Fetur a Nijeriya, NNPC, ya bayyana cewa, sashensu na rarraba man fetir ga 'yan kasuwa masu sari ya fara kwana yana aiki domin tabbatar da an sallami dukkan motocin dakon man da suka zo ɗaukar man. Daraktan Zartaswa na ɓangaren rarraba man na Kamfanin NNPC ɗin, Adetunji Adeyemi shi ya bayyana wa 'yan jarida hakan a Abuja. Inda ya ƙara da cewa, a yanzu haka kusan lita biliyan biyu da kusan rabi na man fetur za a shigo da shi ƙasar nan kafin nan da ƙarshen…
Read More
Manyan ƙalubalen da suke gaban bankunan Nijeriya a 2022

Manyan ƙalubalen da suke gaban bankunan Nijeriya a 2022

Daga AMINA YUSUF ALI Rahotanni sun bayyana cewa, dole bankunan Nijeriya su ƙara zage damtse don tunkarar ƙalubalen da suke tunkaro su a cikin shekarar nan ta 2022.  Ƙalubalen da suke fuskantar bankunan sun haɗa da rashin samun riba sosai, matsanancin haraji, gasa daga kamfanonin sadarwa, da kuma kamfanonin ba da rance. Waɗannan su ne ake ganin za su iya zama barazana ga Bankunan Nijeriya a shekarar nan.  Waɗannan bayanai suna ƙunshe ne cikin rahoton da Renaissance Capital ta rawaito.  Renaissance Capital kamfani ne na kasuwanci da al'amuran banki.  A cewar majiyar tamu, bankunan Nijeriya ba su taɓa shiga cikin…
Read More
Kantinan sayar da abincin ƙasar Sin sun bunƙasa fiye da gabanin ɓarkewar annobar COVID-19

Kantinan sayar da abincin ƙasar Sin sun bunƙasa fiye da gabanin ɓarkewar annobar COVID-19

Daga AHMAD FAGAM Masu hikamar magana na cewa, “sai da ruwan ciki ake jan na rijiya.” Haƙiƙa abinci shine ginshiƙin rayuwar duk wata halitatta a doron ƙasa, kuma rayuwa ba ta yiwuwa ba tare da abinci da kuma abin sha ba. A ƙasar Sin fannin abinci wani babban jigo ne da shugabanni da mabiya ke ɗora muhimmanci kansa. Alal misali, ko da a ƙarshen wannan mako, wani rahoto ya bayyana cewa, kamfanonin dake mallakar kantinan sayar da abinci sun samu gagarumar bunƙasuwar da ta kai matsayin koli wacce har ma ta zarce makamancin lokacin gabanin ɓarkewar annobar COVID-19. Rahoton kan…
Read More
Asarar Dala biliyan 27.8 ta ruguzo da Zuckerberg daga sahun attajirai 10 na Duniya

Asarar Dala biliyan 27.8 ta ruguzo da Zuckerberg daga sahun attajirai 10 na Duniya

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai mawallafin dandalin Fesbuk, wanda yanzu ya koma Meta, Mista Mark Zuckerberg, ya ruguzo daga sahun attajirai 10 mafiya kuɗi a duniya, inda ya ruguzo i zuwa mataki na 12.  Wannan ragin matsayi na Zukerberg ya faru ne a sanadiyyar asarar da kamfanin nasa na Fesbuk ya yi har ta Dalar Amurka Biliyan 27.8 a tsakanin kwana biyu kacal.  Rahotanni sun bayyana cewa,  asarar ta biyo bayan tsame hannayensu da wasu masu hannun jari suka yi daga kamfanin. Al'amarin kuma ya faru bayan kwana biyu kacal da Zukerberg ɗin ya samu ɗarewa kan muƙamin matsayin…
Read More
Bunƙasa lantarki: Nijeriya za ta karɓi rancen Dala miliyan 200 daga Japan

Bunƙasa lantarki: Nijeriya za ta karɓi rancen Dala miliyan 200 daga Japan

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnati Tarayyar Nijeriya ta bayyana ƙudurinta na amso rancen Dalar Amurka Miliyan 200 daga hukumar haɗakar kamfanoni  na ƙasar Japan (JICA). Gwamnatin ta bayyana cewa, ba wani abu za ta yi da kuɗaɗen ba illa ta ƙara ƙarfin wutar lantarki a wasu zaɓaɓɓun ɓangarori a cikin jihohin Ogun da Legas. Alhaji Abubakar Aliyu, Ministan Makamashin Nijeriya, shi ya bayyana haka, a yayin da yake amsar baƙuncin wasu wakilai daga hukumar ta JICA a ofishinsa dake birnin tarayyar Abuja, inda ministan ya ƙara da cewa, wannan yunƙuri an yi shi ne domin a ƙara inganta sashen samar da…
Read More
Kotu ta tursasa wa kamfani cigaba da biyan albashi ga korarren ma’aikaci

Kotu ta tursasa wa kamfani cigaba da biyan albashi ga korarren ma’aikaci

Daga AMINA YUSUF ALI Wata kotun masana'antu reshen garin Fatakwal ta tursasa wa wasu kamfani mai suna, Hughes Limited da Baker Hughes Incorporated su cigaba da biyan ma'aikacinsu, Joshua Umoren albashi duk bayan sati biyu a tsahon shekaru domin biyan haƙƙoƙinsa.  Alƙalin kotun, Mai Shari'a Zainab ta yanke hukuncin a zaman kotun na ranar Juma'ar da ta gabata, bayan ta kammala sauraren shaidu daga ɓangarorin lauyoyin guda biyu. Wato na wanda ake ƙara, da na wanda yake ƙarar.  Alƙalin ta bayyana cewa, kamfanonin ba su karya doka ba don sun sallami Josua daga aiki ba. Amma sun karya dokar aiki…
Read More
Abinda ya sa Shoprite ya rufe reshensa na Legas

Abinda ya sa Shoprite ya rufe reshensa na Legas

Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin rukunin shagunan sayayya na Shoprite ya rufe reshensa na unguwar Maryland da yake a jihar Legas.  Haka kuma rahotanni sun sake bayyana cewa, kamfanin ya sanar da cewa, nan ba da daɗewa ba zai buɗe sababbin rassansa a garuruwan Kaduna, Fatakwal, Binin, da kuma Jos a ƙoƙarinsa na ganin ya bunƙasa kasuwancinsa. Shi dai kamfanin 'The Retail Supermarket Nigeria Limited (RSNL)' wanda shi ne mamallakin rukunin shaguna na Shoprite, ya ba da sanarwar rufe reshen nasa na Maryland a Ikejan jihar Legas  a ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2022 da muke ciki.  Ciyaman ɗin…
Read More
Nijeriya ta amince Kamfanin jiragen Emirates su koma aiki a ƙasar

Nijeriya ta amince Kamfanin jiragen Emirates su koma aiki a ƙasar

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Najeriya ta amince jiragen kamfanin sufurin jirgin sama na Emirates da ke Dubai su koma jigila a ƙasar kowane lokaci daga yanzu. A yayin da kamfanin jirgin Air Peace da ke Nijeriyar shi ma ya ce zai koma safara zuwa Dubai, daga ranar1 ga watan Maris na 2022. Sanarwar tana ƙunshe ne a wata wasiƙa da Hukumar Kula da Sufurin Jirgin Sama ta Najeriya (NCAA) mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Captain Musa Nuhu ta rubuta wa shugaban hukumar sufurin jirgin sama ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Saif Mohammed Al Suwaid. A wasiƙar, hukumar ta Najeriya…
Read More