USAID ta bada tallafi ga manoman rogo 100 a Kwara

Daga AMINA YUSUF ALI

Kimanin ƙananan manoman rogo guda 100 ne dai ‘yan asalin jihar Kwara suka samu tagomashin tallafi daga ƙungiyar tallafi ta Amurka (USAID) don bunƙasa harkar noma. 

An zavo waɗannan manoman rogo ne daga ƙananan hukumomin jihar Kwara. Inda aka fara da ba su kayan aiki da kuma horaswa a fannin noman zamani domin ingantawa da bunƙasa sana’arsu. 

Mashiryin shirin ba da tallafin jarin ga manoman rogon, Mista Banjo Famuyiwa, ya bayyana cewa, wannan shirin USAID a Nijeriya ce ta ɗauki nauyinsa tare da haɗin gwiwar AYOSIFAM da ma’aikatar faɗaɗa aikin noma da raya karkara ta jihar ta Kwara.

Mista Famuyiwan ya yi wannan yayin jawabin nasa ne  jim kaɗan bayan an kammala rabon kayan aiki ga manoman rogon waɗanda suka fito daga ƙananan hukumomin  Kudancin Illorin, da Moro, da Ifelodun, Irepodun da kuma Asa a ƙarshen satin nan da ya gabata a Jihar.

Ya ƙara da cewa, manoman rogo sun zama su ne ƙashin baya wajen samar da kayan aiki ga masana’antun da suke samar da garin rogo (garin kwaki). Kuma a cewar sa annobar Kwarona ba ƙaramin lahani ta yi wa manoman ba. Don haka a cewar sa, suna neman tallafi yadda za a cicciɓa su su farfaɗo. 

Ya ƙara da cewa, sannan manoman suna buƙatar su samu kare rayuwarsu da lafiyarsu daga illolin maganin ƙwari da kuma wasu haɗurran a sana’arsu. Don haka bayan tallafin kuɗin, USAID ta ba da kayan aiki ga ƙananan manoman rogo ga manoman ƙanann hukumomin Ilorin ta kudu, da Moro, da Ifelodun, da Irepodun da Asa an a jihar Kwara. Inda kowanne manomi ya samu hular malafa guda, da takalmin roba, da riga biri da wando saboda kariya. 

Manoman da suka samu tagomashin da ma tuni an ba su horaswa tun a watan Nuwambar shekarar bara. Sannan a watan Disambar dai ta bara aka buɗe musu wata turakar yanar gizo mai suna www.ayosifamhub.com.ng domin su dinga tallata amfanin gonarsu ga masu buƙata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *