Matsalar garkuwa da mutane laifin gwamnonin Arewa ne, inji Miyetti Allah

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Matsalar da ake fama da ita a arewacin Nijeria ta fuskar garkuwa da mutane da satar dabbobi da rashin zaman lafiya laifin gwamnonin Arewa ne, inji shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Alhaji Bello Muhammed Baɗejo a lokacin da ya je ziyarar aiki ta kwana ɗaya a cikin wannan makon.

Baɗejo ya ci gaba da cewar gwamnonin Arewa su ne suka gaza wajen inganta rayuwar Fulani makiyaya ta fuskar samar masu da kayan more rayuwa da tsunduma su cikin harkokin Fulani makiyaya.

Ya ce rashin kulawar gwamnonin Arewa a kan Fulani makiyaya shi ne ya sa gwamnonin kudanci suka samu damar yi wa Fulani kisan gilla kuma suke wa arewan da ‘yan Arewa kallon banza ba sa ganin kan kowa da gashi.

Ya kuma shawarci Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar da ya ci gaba akan ƙoƙarinsa na samar da ayyukan inganta rayuwar ‘ya’yan Fulani makiyaya ta hanyar samar da makiyayu da makarantu da asibitoci da ruwan sha don inganta rayuwar makiyaya.

Ya kuma buƙaci sauran gwamnonin Arewa da su yi koyi da Gwamna Badaru domin ya zama abin koyi a faɗin Nijeriya wajen inganta rayuwar Fulani makiyaya, Badaru ne gwamna na farko a faɗin Nijeriya da ya samar da burtalin makiyaya da fanfunan bada ruwan sha a makiyayu tare da gina makarantun ‘ya’yan Fulani a faɗin Nijeriya.

Ya ci gaba da cewar da a ce sauran gwamnonin Arewa sun yi abinda Gwamna Badaru ya yi wa makiyaya da ba a samu kai a cikin halin da ake ciki ba na damuwa; amma rashin kulawa na wasu mahukunta shi ne ya jefa Fulani a halin da suke ciki.

Ya ce rayuwar Fulani ta ta’azzara kuɗin ceton lafiyarsu daban yake a kotuna shari’arsu daban take a caji ofis, hukuncinsu daban yake ba a yi masu adalci ba a basu dama wajen aikin gwamnati da harkokin siyasa. Haka ne ya sa Fulani faɗawa cikin wancan hali na yin garkuwa da mutane da sace-sacen dabbobi.

Baɗejo ya ce sauran gwamnonin arewa ba su da gaskiya suna amfani ne da sunan Fulani makiyaya wajen cimma burinsu na siyasa, shi ya sa ba sa son wannan rikicin ya ƙare.

 Ya ce matuƙar gwamnonin suna buƙatar kawo ƙarshen al’amarin abu ne mai sauƙi kuma mai yiwuwa.