Nijeriya 2023: Birnin Daura ya tumbatsa da fastocin takarar Amaechi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

A Kwanakin baya ne Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk ya yi addu’ar Ministan sufuri na Nijeriya, Rotimi Amaechi, wanda ya bayyana shi da mai nasara kan dukkan abinda ya sanya a gaba, Allah ya ba shi wani matsayi fiye da wanda yake a kai.

Shahararren sarkin dai ya yi wannan addu’a ce yayin da yake karrama Minista Amaechi da sarautar gargajiya ta Ɗan Amanar Daura, wanda yake nufin amintaccen ɗan Daura.

Bikin naɗin na Ɗan Amanar Daura ya samu halartar fitattun mutane daga sassa daban-daban na ƙasar nan, haɗi da waɗanda suke yi masa yaƙin takara ya zama shugaban ƙasa a zaɓen shekara ta 2023, yayin da suka cike garin Daura da hotunan Amaechi waɗanda aka daje su da rubutuce-rubucen ‘Amaechi ya tsaya takarar shugabancin ƙasa’.

Sarkin na Daura ya ce, “mun hallara ne a wannan rana ta yau domin mu rama kirki da soyayya da ministan sufuri, Chibuke Rotimi Amaechi ya nuna mana da kyakkyawar zuciya.

“Saboda haka, ya zame wajibi wa masarautar Daura ta nuna mutunci da aka yi mata. Addu’a ita ce Allah ya baka babban ofishi fiye da wanda kake ciki a halin yanzu.”

Faruk ya bayyana cewar, masarautar Daura ta karrama Amaechi da sarautar gargajiya ne saboda gudunmawar sa ga walwala da tattalin arzikin masarautar, musamman bisa ƙoƙarin sa na tabbatar da kafuwar Jami’ar Nazarin Lamuran Sufuri a garin Daura, haɗi da gina hanyar dogo wacce ta taso daga birnin Kano, ta ratsa garin Daura zuwa garin Maraɗi ta ƙasar Nijar.

“Ba mu bayar da sarautar gargajiya ga mutum saboda attajirancin sa. Mun ba ka wannan sarauta ne bisa ƙwazo da sadaukartakarka waɗanda suke da tasiri ga rayuwar jama’ar karkarar mu, da ma ɗaukacin ‘yan Nijeriya baki ɗaya,” kamar yadda sarkin ya ce.

Bikin karramawar, ya haɗa da naɗin wani babban jigo a jam’iyyar APC, Nasiru Haladu Danu wanda aka ba shi sarautar ‘Tafida Baba’. Daga cikin rukunin jama’a da suka halarci bikin naɗin, sun haɗa da wani gungu da suke nema wa Amaechi goyon baya masu laƙabin ‘Amaechi ya tsaya takarar neman shugabancin Nijeriya, waɗanda a turance sune ‘Amaechi for President in 2023, ‘Frontier for Peace and Unity (FPU), ‘Amaechi Vanguard, ‘Amaechi 2023 Agenda da ‘Northern Grassroots Mobilization’.

Bikin naɗin na Minista Amaechi ya samu halartar Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, Ooni Sarkin Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, Alhaji Muhammadu Nuhu Sanusi (Sarkin Dutse), Erin Edet Ekong (Shugaban Majalisar Sarakuna ta jihar Kuros Ribas, Abdullahi Lamido Sunusi (Magajin Garin Kano), Chukwuemeka Nwajiuba (Ƙaramin Ministan Ilimi),  Ministan Kiwon Lafiya, Olorunnimbe Mamora.