Abinda ya sa Shoprite ya rufe reshensa na Legas

Daga AMINA YUSUF ALI

Kamfanin rukunin shagunan sayayya na Shoprite ya rufe reshensa na unguwar Maryland da yake a jihar Legas. 

Haka kuma rahotanni sun sake bayyana cewa, kamfanin ya sanar da cewa, nan ba da daɗewa ba zai buɗe sababbin rassansa a garuruwan Kaduna, Fatakwal, Binin, da kuma Jos a ƙoƙarinsa na ganin ya bunƙasa kasuwancinsa.

Shi dai kamfanin ‘The Retail Supermarket Nigeria Limited (RSNL)’ wanda shi ne mamallakin rukunin shaguna na Shoprite, ya ba da sanarwar rufe reshen nasa na Maryland a Ikejan jihar Legas  a ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2022 da muke ciki. 

Ciyaman ɗin kamfanin,  Tayo Amusan, ya bayyana wa Jaridar PREMIUM TIMES ta Turanci a yayin zantawarsa da wakili daga jaridar. Inda ya bayyana cewa, sun yanke wannan shawara ta rufe reshen nasu ba don suna so ba. Sai don ya zama wajibi su tattara ya nasu ya nasu su garƙame reshen nasu. 

A ƙarshe ya ce yana gode wa al’ummar Legas da kewaye wajen gudunmowa da kuma ciniki da suka yi musu, kuma suna sa ran nan gaba su sake yin hulɗar ciniki da su. 

Haka kuma a wasu rahotannin an bayyana cewa, kamfanin zai sake buɗe reshensa na Jakande, a dai jihar Legas ɗin bayan kusan shekaru biyu da rufe shi sakamakon ta’annatin da wasu ɓata garin suka yi na yi musu sata da fashi tare da fakewa da zanga-zangar EndSARS suka yi a Oktobar shekarar 2020.