Rasuwar Garba Aliyu Zariya ta girgiza duniyar ’yan jarida

Daga DAUDA USMAN a Legas

A ranar Asabar ɗin ƙarshen makon jiya ne, Allah ya karɓi rayuwar fitaccen ɗan jarida, Alhaji Garba Aliyu Zariya. 

Wannan bawan Allah ya rasu ne da da misalin ƙarfe 12:00 na dare a gidansa da ke unguwar Agege ta Jihar Legas. 

Tuni dai aka rigaya aka yi jana’izarsa, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, tare da fatan Allah ya jiƙan sa, ya kuma gafarta masa da rahama.

Shi dai Marigayi Alhaji Garba Aliyu Zariya an haife shi a ranar 8 ga Janairu, 1969, wato shekaru 63 kenan da suka gabata.

Garba Zariya ya rasu ya bar mace ɗaya da ‘ya’ya shida (maza biyu da mata huɗu). Daga cikinsu akwai, Aliyu Garba Aliyu, wanda ya ke karatu a makarantar koyan aikin sojan ruwa, sai Hauwa’u Garba Aliyu, ma’aikaciya a gidan Rediyon VON FM da ke Birnin Legas. 

Haka kuma Marigayi Garba Aliyu ya taɓa aikin jarida a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, inda gidan rediyon ya tura shi Maiduguri, domin ya wakiltar sa a can jihar ta Borno. A yayin da a can ma ya samu muƙamin shugaban ƙungiyar ‘yan jaridu ta Jihar Borno, ida daga nan aka maida shi Jihar Ondo, daga Ondo kuma aka dawo da shi Jihar Ogun.

Daga nan sai aka kai marigayin Jihar Legas, inda a nan Legas ɗin ma ya ɗauki tsawon lokaci yana wakiltar Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna.

Sannan Kuma  ya ajiye aikinsa da Rediyon Nijeriya Kaduna ya koma Rediyon Faransa, inda a nan ma ya samu muƙamin Mataimakin Edita gabaɗaya, wanda yana kan wannan matsayi ne, Allah ya karɓi rayuwarsa. Da fatan Allah ya gafarta masa.

Ahmed Isa Koko, fitaccen ɗan jarida a Legas kuma shugaban gidan Rediyon VON FM, ya bayyana cewa: rasuwa irin ta su marigayi Garba Aliyu Zariya  rashi ne da ya shafi ƙasa gabaɗaya.

Hakazalika, Jamilu Umar Matazu, wakilin Mujallar Muryar Arewa, kuma makusanci ga marigayin kafin rasuwarsa, ya ce, rasuwar Marigayin Alhaji Garba Zariya rashi ne da ya girgiza shi, ya ma girgiza al’ummar jihar Legas bakiɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *