Laifin Gwamnatin Tarayya ne idan muka sake tsunduma yajin aiki – ASUU

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) Reshen Jihar Legas ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tunkari Gwamnatin Tarayya gar-da-gar a kan matsalar da ke damun jami’o’in gwamnati, waɗanda su ke tilasta tafiya yajin aiki.

ASUU ta ce, ƙungiyar ta na tafiya yajin aiki ne sai bayan ta yi iyakar dukkan ƙoƙarin sasantawa, amma abin ya faskara.

Idan ba a manta ba, ASUU ta nemi mambobin ta su ware rana ɗaya domin wayar wa ‘yan Nijeriya kai cewa su na ja-in-ja da gwamnati ne domin su ceto jami’o’in ƙasar nan daga durƙushewa.

ASUU ta ce har yau Gwamnatin Buhari ta ƙi cika alƙawarin da ta ɗauka cikin 2020, wanda ɗaukar alƙawarin ne ya sa ASUU ta janye yajin aikin da ya shafe watanni 9 su na yi.

A jawabin sa yayin taron ganawa da manema labarai a Jami’ar Legas da ke Akoka, a ranar Talata, Shugaban ASUU na Legas, Adelaja Odukoya, ya ce rashin cika alƙawarin da gwamnatin Buhari ta yi lokacin da ta lallashe su har suka janye yajin aikin watanni 9 cikin 2020, shi ne zai sake haddasa masu tafiya wani yajin aikin.

“Don haka a tuhumi Gwamnatin Tarayya, laifin ta ne na rashin cika alƙawari idan mu ka sake tafiya wani yajin aiki, wanda babu makawa sai mun tafi nan gaba kaɗan, kwanan nan,” inji shi.

Cikin makon jiya ne Buhari da shugabannin addinai sun yi wa malaman jami’a magiya kada su tafi yajin aiki.

Shugaba Muhammadu Buhari ya roƙi Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) cewa Gwamnatin Tarayya za ta cika alƙawurran da ta ɗaukar masu, amma su yi wa Allah su yi wa Annabi kada su tafi yajin aiki.

Ya ce yajin aikin zai dagula zangon karatun ɗalibai. Buhari ya ce gwamnatin sa za ta ƙara danƙara maƙudan kuɗaɗe domin inganta tsarin ilmi.

Buhari ya yi wannan alƙawari a lokacin da ya karɓi baƙunci Ƙungiyar Shugabannin Addinai, a ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar da Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa (CAN), Samson Ayekunle.

A ranar Juma’a ce dai ASUU ta zargi Gwamnatin Tarayya da cewa ba ta iya cika alƙawurran da ta ke ɗauka a baya, ba. Kan haka ne ASUU ta ce Gwamnatin Tarayya ta ƙware wajen iya faɗa-ba-cikawa.

Amma kuma da Buhari ke magana, ya ce duk al’ummar da ke fatan ci gaba da kuma alheri, ba za ta yi wasa da harkokin ilmi ba.