Gasar Amurka, gasa ce cikin lumana ko yunƙurin hana bunƙasuwar sauran ƙasashe?

Daga CRI HAUSA

Kwanan baya, majalisar dokokin ƙasar Amurka ta zartas da Dokar Gasa ta Amurka ta Shekarar 2022, domin tabbatar da matsayin ƙasar na kan gaba a fannonin masanaantu, ƙirƙire-ƙirƙire, da ƙarfin tattalin arziki. Amma, cikin wannan doka, ƙasar Amurka ta yi suka kan manufofin ƙasar Sin wajen neman ci gaba, da wasu harkokinta na cikin gida. Haƙiƙa dai, nufinta shi ne hana ci gaban ƙasar Sin bisa hujjar yin gasa. Shi ya sa, ake ganin cewa, wannan dokar da ƙasar Amurka ta fidda, doka ce ta hana ci gaban sauran ƙasashe.

Ƙasar Amurka tana da yancin neman bunƙasuwa, amma, ba ta hanyar hana bunƙasuwa da ɓata sunan ƙasar Sin ba, balle ma, tsoma baki cikin harkokin gidan ƙasar, da kuma ɓata moriyarta.

Shirin ƙarfafa dangantakar dake tsakanin ƙasar Amurka da lardin Taiwan na ƙasar Sin, da aka ambata cikin wannan doka, ya keta manufar ƙasar Sin ƙasa daya tak, da kuma ƙaidar sanarwoyin haɗin gwiwa guda uku da aka ƙulla tsakanin ƙasar Sin da da ƙasar Amurka. Lamarin da ya nuna cewa, wasu yan siyasar ƙasar Amurka suna neman hana bunƙasuwar qasar Sin baki ɗaya, ta hanyar ɓata yanayin siyasa a yankin Taiwan na ƙasar.

Amma, ƙasar Amurka ba za ta cimma nasarar mugun burinta ba, domin, tabbas, ƙasar Sin za ta mai da martani ga waɗanda suka tsoma baki cikin harkokin gidanta, da kuma neman ɓata moriyarta. Da fatan ƙasar Amurka za ta iya dakatar da wannan doka nan take, da kuma daidaita dangantakar dake tsakaninta da ƙasar Sin da idon basira.