Matuƙin adaidaita ya halaka ɗan yuniyal kan Naira 20 a Keffi

Daga BASHIR ISAH

A ranar Juma’a ta makon jiya wani matuƙin adaidaita-sahu ya yi ajalin wani jami’in yuniyal na NURTW mai suna Abba da ke aiki a tashar motar da ke kusa da NTA, hanyar Abuja a Keffi, jihar Nasarawa.

Matuƙin keken ya halaka Abba ne ta hanyar daɓa masa wuƙa har sau biyu biyo bayan jayayyar da ta shiga tsakaninsu a kan rashin biyan kuɗin sallamar da ‘yan yuniyal suka saba karɓa daga hannun duk wani mai abin hawan da suka ba shi fasinja a tasharsu.

Da yake yi wa wakilinmu ƙarin haske kan yadda lamarin ya auku, Aƙilu Mu’azu wanda jami’in yuniyal ne a nan tashar da lamarin ya faru ya ce, “Marigayin ya buƙaci mai keken ya biya kuɗin sallama Naira 20 kasancewar an ba shi fasinja, sai ya ce ba zai biya ba. Daga nan sai jayayya ta shiga tsakaninsu, kawai sai ya zaro wuƙa ya daɓa wa Abba a zuciya.”

Mu’azu ya ce, “nan take wanda aka daɓa ma wuƙa ya ce ga garinku nan. Da ‘yan sanda suka zo ne suka ɗauke shi suka tafi da shi don gudanar da bincike.

Binciken Manhaja ya gano cewa, bayan aukuwar lamarin, abokan aikin marigayin sun kama mai keken yayin da ya yi yunƙurin tserewa, kana aka miƙa shi ga ‘yan sanda.

An ga yadda abokan aikin marigayin suka banka wa keken wanda ya kashe musu ɗan’uwa wuta suka ƙona shi ƙurmus.

Ya zuwa haɗa wannan rahoto, batun na gaban ‘yan sandan Keffi don yin abin da ya kamata, kuma an miƙa gawar Abba ga ‘yan’uwansa don yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.