Allah ya jiƙan Rayan Awram

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A yayin da har yanzu ake cigaba da juyayin rasa yarinya ’yar shekara 5 da haihuwa da malamin makarantarsu, Abdulmalik Tanko ya yi wa kisan gilla a Kano, sai ga wani juyayin na rasa yaro Rayan Awram mai shekaru 5 shi ma a Maroko. Abin da ya bambanta rashin yaran biyu shi ne, yayin da na Hanifa cin amanar da malmanin makaranta ya yi ne bayan sacewa da neman kuɗin fansa ya kuma kashe ’yar yarinya wai don kar asirinsa ya tonu; mutuwar Rayan kuma sanadiyyar hatsarin da ya rutsa da shi ne lokacin da ya ke wasa a garin su da ke arewacin ƙasar Maroko inda ya faɗa rijiya mai zurfin ƙafa 100 da ta ke tsukakkiya.

An samu kwana uku ana ta gwagwarmayar ceto yaro Rayan amma abin bai samu nasara cikin sauƙi ba don matsin da rijiyar ke da shi inda babban mutum ba zai iya shiga ba. Jami’an ceto sun yi amfani da dabarar tona wani ramin a gefe don ya jagorance su har inda Rayan ya ke don fito da shi daga wannan hali mai ban tausayi. Yanayin wajen mai duwatsu da ƙasa ya sa sai an bi aikin a hankali don gudun ruftawar ƙasa ko ma girgizar ƙasa a bigiren. Haka nan jami’an sun zura ruwan sha da iskar shaka ‘OXYGEN’ don taimaka wa yaron. Kazalika an zura kamara inda ta ɗauko hannun yaron ya na kwance ta gefen jikin sa. A duk lokacin aikin ceton mai wuyar gaske ba a tantance ko yaron ya iya amfani da ruwan da a ka zura ba. Dubbban mutane sun taru a wajen su na addu’a da ƙara wa jami’an agajin ƙarfin gwiwar taƙarƙarewa kan wannan muhimmin aikin ceton. Mutanen kan yi kabbara da fatar Allah ya hukunta fito da yaron nan da ran sa.

’Yan mitocin ƙarshe zuwa inda yaron ya ke su ka fi hatsari don gudun ruftawar ƙasa da ka iya kawar da farin cikin samun yaron cikin salama. A gaskiya mutane sun kasance cikin zullumi kuma ba a bigiren ko ƙasar Maroko kaɗai ba, hakan ya shafi dukkan sassan duniya ne da ke bin labarin aikin ceton sau da ƙafa. An riƙa nuna yadda a ke gudanar da aikin a gidajen talabijin da zantawa da shugaban tawagar aikin ceton da ta haɗa da likitoci da ke cikin shirin kiftawa da bismillah na tallafawa lafiyar yaron nan. A cikin ikon Allah da ƙaddarawarsa, ƙarshe an samu an fito da Rayan da dama a ka tsara motar ɗaukar marar sa lafiya da jirgi mai saukar angulu don garzayawa da shi asibiti a ceto ran sa, amma Allah ya karɓi abunSa, rai ya yi halin sa. Dole zullumin da mutane ke ciki ya juye ya koma zubar da hawaye da yi wa juna ta’aziyyar rashin wannan ƙaramin yaro. Haƙiƙa mutane sun yi matuƙar kaɗuwa da wannan abin juyayi. Jikin jami’an agajin ya yi lakas don ganin duk ƙoƙarin ɗan Adam sai yadda Allah mahaliccin sammai da ƙassai ya hukunta. Duk lokacin ka ke aikata wani aiki, ka na jiran hukuncin Allah ne ya biya ma ka muradun ka masu kyau. A duk kuma lokacin da hukuncin Allah ya zo sai a karɓe shi hannu bibbiyu da maida komai gare shi don shi ne mai bayarwa ga wanda ya so ya kuma karɓe daga hannun wanda ya so. Ɗan Adam na tafiya a doron ƙasa ne ba tare da ya san gaibu ba.

Babban darasin da ke cikin hatsarin da yaron nan ya faɗa shi ne yadda mutane su ka haɗa kai su na addu’a don neman taimakon Allah ga ceto yaro Rayan daga rami mai zurfi. Dubban mutane ne da kawai abun da za a ce sun sani shi ne yaro ne ƙarami da bai yi wa kowa laifi ba ya faɗa wannan hatsari. Na tabbata mutane na ƙaddara cewa yaron tamkar ɗan su ne don haka su ka saka takalman mahaifansa wajen shiga tsananin juyayi don ganin an ceto shi. Irin wannan haɗin kan ake nema a ko ina a duniya.

Irin wannan taro da samun manufa mai kyau a ke so tsakanin wanann gari da wancan, tsakanin wannan addinin da wancan, tsakanin ƙasar nan da ƙasar can, tsakanin nahiyar nan da nahiyar can. Da za a samu nasarar mutanen duniya su haɗa kai irin yadda dubban mutane su ka taru don ceto marigayi Rayan, da kuwa an samu zama mai kyau. Haƙiƙa irin wannan zama a ke buƙata tsakanin makwabta. Lallai fa da mutane za su so juna irin na darasin Rayan da zai zama ba mai kwana bai ci abinci ba ko bai sha ruwa ba. Gaskiya ni a na wa hangen inda za a samu ƙarfafa irin wannan gamayya za a iya cimma nasarar rage kasahe-kashen rayuka ta hanyar zalunci a duniya. Hakan zai sa gwamnatoci su zama masu adalci yayin da waɗanda a ke mulka za su riƙa yi wa shugabanni fatar alheri. Ka ga akasin hakan ake samu don yawancin jama’a kan rayu ne tamkar zaman ’yan marina kowa da inda ya ke kallo. Ba ma a marina ba kawai, ai yanzu za ka ga mutum ya na neman taimako kuɗin magani don ceto ransa a asibiti amma zai yi wuya ya samu. Wasu ba sa iya tunkarar asibitin da za a iya kula da su don rashin kuɗin da za su biya magani don haka sai su zauna a gida ko su aika a sayo mu su ’yan magunguna a ɗakin magani su zubawa hukuncin Allah ido. Yanzu fa ba ma abun mamaki ba ne a wannan zamani don rashin kuɗi mutum ya zauna a gida a na kula da shi da ganyen dalbejiya kuma ba mamaki cutarsa na buƙatar aiki na tiyata ne daga ƙwararren likita. Mutum ba zai san yadda asibitoci su ka zama waje na ɗawainiya ba sai in mutum ya gamu da jinya da ala tilas ya na buƙatar kulawa ta musamman.

Yayin da masu damar inshorar lafiya ke samun rangwame, waɗanda ba su da damar kuma ba su da abin biya kan shiga halin ni ’ya su da gwammacewa su kira likitan unguwa ya zo ya yi mu su ƙarin ruwa a gida. Idan hukumomi da jama’ar kowane yanki na da tsarin taimakawa juna ta hanyar kafa wani asusu da za a riƙa kula da mutanen da ba su da ƙarfin tattalin arziki, da haƙiƙa an samu sauƙi, kuma irin wannan sauƙi kan samar da haɗin kai, shi kuma haɗin kai kan samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ƙaruwar arziki. Zai yi kyau al’umma ta koyi darasi daga jama’ar Rayan wajen kafa ƙungiyoyin taimakon kai da kai a dukkan unguwanni don agaza wa juna a lokacin buƙata.

Ana wanke tukunya don abincin gobe kuma masu azancin zance kan ce ba a fafa gora ranar tafiya. Duk abin da a ka shirya kafin isowar sa za a iya samun maslaha ko sauƙi. Kamar bin dokokin Allah ne tsakani da Allah a duniya kan zama jarin ranar gobe kiyama. Sau da dama talakawa kan gaza bin wannan tsari na ajiya maganin wata rana sai ka ga buƙatar ragon suna ko na laiya ya na gagarar su don in sun samu dan kaɗan da su ke gani ba a ajiye mafi karanta a ciki don amfanin buƙatar gobe. Na taɓa ji a na cewa da kaɗan-kaɗan kogi ya cika har a kasa ganin tsawonsa daga gaɓarsa. Rayuwa ta zama tashi in taimake ka ne. Ka da kowa ya kwanta ya jira sai an yi ma sa ɗauki kafin taɓuka abin kirki. Idan kowa zai miƙe don samar da mafita, za a iya samun sauƙin rayuwa.

Na lura a shekarun baya haɗin kan mutanen mu kan taso ne lokaci ɗaya kacal wato in a na gasar ƙwallon ƙafa ta Afirika ko ta kofin duniya. Za ka ga mutanen mu ba bambancin wani bambanci sun taru su na mara baya don a ɗauko kofi. Ko a kwanan nan na ga irin wannan haɗin kan na wucin gadi a gasar ƙwallon ƙafa da ka yi ta neman kofin Afirika a Kamaru. Mutane sun taru su na mara baya ga ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasa don a samu nasarar kawo kofi gida. Idan a ka sha kallo za ka ji an yi ihu na nuna murnar nasarar da a ka samu. Idan kuma a ka sha gida za ka ji tsit a gari kowa na cikin zullumi don rashin sanin yadda sakamakon ƙarshe zai kaya.

Abin takaici da ya ke neman wargaza wannan haɗin kan shi ne ƙabilanci ko ɓangaranci da kan taso a yayin da ba a samu nasara ba. Sai ka ga an duba wanda a ke tsammanin laifin sa ne rashin nasarar, sai a ce don dan waje kaza ne ya sa ba a samu nasara ba ko don rashin saka wane na gefen ƙasa kaza ne da fi iyawa ya sa a ka sha kaye.

Duk abin da zai kawo gyara da farfaɗo da wannan haɗin kan da karsashi na ƙasa shi ne adalci. Idan an ba wa mutum amanar wani aiki to ya yi gaskiya ta hanyar rufe ido da rashin la’akari da son zuciya wajen ɗaukar matsaya.