Asarar Dala biliyan 27.8 ta ruguzo da Zuckerberg daga sahun attajirai 10 na Duniya

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin yanzu dai mawallafin dandalin Fesbuk, wanda yanzu ya koma Meta, Mista Mark Zuckerberg, ya ruguzo daga sahun attajirai 10 mafiya kuɗi a duniya, inda ya ruguzo i zuwa mataki na 12. 

Wannan ragin matsayi na Zukerberg ya faru ne a sanadiyyar asarar da kamfanin nasa na Fesbuk ya yi har ta Dalar Amurka Biliyan 27.8 a tsakanin kwana biyu kacal. 

Rahotanni sun bayyana cewa,  asarar ta biyo bayan tsame hannayensu da wasu masu hannun jari suka yi daga kamfanin.

Al’amarin kuma ya faru bayan kwana biyu kacal da Zukerberg ɗin ya samu ɗarewa kan muƙamin matsayin mutum na tara mafi arziki a duniya. Sai ga shi kwanaki biyu kawai a tsakani, a rahoton kasuwar jari ta ‘Newyork Stock’ an bayyana shi a matsayin na 12, domin a yanzu haka, ƙarfin arzikinsa Dalar Amurka 86.7 ne kawai, wanda ko a watan Oktoban bara, ƙarfin arzikin nasa ya kai Dalar Amurka 134.5.

A yanzu haka dai, Zukerberg yana ƙasa da biloniyan Ba’indiyen nan, Mista Mukesh Ambani, wanda a yanzu haka ƙarfin arzikin Ambani ya kai Dalar Amurka Biliyan 90.