Daga AHMAD FAGAM
Masu hikamar magana na cewa, “sai da ruwan ciki ake jan na rijiya.” Haƙiƙa abinci shine ginshiƙin rayuwar duk wata halitatta a doron ƙasa, kuma rayuwa ba ta yiwuwa ba tare da abinci da kuma abin sha ba.
A ƙasar Sin fannin abinci wani babban jigo ne da shugabanni da mabiya ke ɗora muhimmanci kansa. Alal misali, ko da a ƙarshen wannan mako, wani rahoto ya bayyana cewa, kamfanonin dake mallakar kantinan sayar da abinci sun samu gagarumar bunƙasuwar da ta kai matsayin koli wacce har ma ta zarce makamancin lokacin gabanin ɓarkewar annobar COVID-19.
Rahoton kan batun masana’antu ya bayyana cewa, kamfanonin gidajen sayar da abinci na ƙasar Sin sun samu gagarumar bunƙasuwa a shekarar 2021 duk da matsin lambar da annobar COVID-19 ke haifarwa, inda aka samu ƙaruwar buɗe sabbin gidajen sayar abinci da kashi 25.5 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2020.
A bisa rahoton, jimillar sabbin kamfanonin sayar da abinci miliyan 2.36 aka samu a shekarar 2021, kamar yadda babban kamfanin sayar da abinci ta intanet na ƙasar Sin Meituan ya bayyana. Rahoton kamfanin ya ce, ƙasar Sin tana samun ƙaruwar harkokin hada-hadar gidajen sayar da abinci a shekarun baya bayan nan, inda adadin ke cigaba da ƙaruwa daga kashi 12.8 bisa 100 a shekarar 2018 zuwa kashi 15 bisa 100 a shekarar 2020. Har ma an bayyana cewa, fannin masana’antun samar da abincin ƙasar Sin sun mayar da komaɗarsu a shekarar 2021 wanda ya kai matsayin na gabanin ɓarkewar annobar, inda jimillar kuɗaɗen shigar fannin ya ƙaru da kashi 18.6 bisa 100 idan an kwatanta da na shekarar da ta gabata wanda adadin ya kai yuan triliyan 4.69, kwatankwacin dala biliyan 736.
Koda yake, wannan cigaban da ake samu ba zai rasa nasaba da irin jajurcewa da kuma ƙwararan matakai da mahukunta ƙasar ke ɗauka don ganin fannin samar da abinci ya samu gagarumin tagomashi ba. Alal misali, ko da a ƙarshen wannan mako, firaministan ƙasar Sin Li Keqiang, ya jaddada aniyar tallafawa fannin aikin gona domin tabbatar da cigaban bunƙasa samar da hatsi wanda ya zarta kilogram biliyan 650 cikin shekara guda.
A cewarsa, ya zama wajibi a ƙara azama don tallafa wa aikin gona, da bada tabbacin samar da kayan amfanin gona, da tabbatar da daidaita farashin kayan amfanin gonar, da kuma tabbatar da fara ayyukan noman bazara a kan lokaci. Dama dai masu hikimar magana na cewa, “bayan wuya sai daɗi.”
