Taron manyan jami’ai huɗu da Amurka ta kira ya ƙara fallasa manufar Amurka ta tada hargitsi

Daga CRI HAUSA

A baya-bayan nan, ƙasar Amurka ta fitar da rahoton taron ganawar manyan jami’an ƙasashe 4 mai laƙabin “U.S. Indo-Pacific Strategy”, rahoton da ya ƙara tabbatar da manufar Amurka, cikin shekarun baya-bayan nan, ta kambama zargin nan na kasancewar “Sin barazana”, da gayyatar ƙawayen ta domin haɗa wani gungu, da fatan yin haɗin gwiwar daƙile ƙasar Sin, ta yadda Amurka za ta cika burin ta na wanzar da danniya, da farfaɗo da tasirin ta a yankin tekun Asiya da Fasifik, da ma sauran sassan duniya.

Don haka dai ta bayyana a fili, cewa taron manyan jami’an na Amurka, da Australia, da India, da Japan, na cike da salon cacar baka, da siyasar wariya.

Ɓangaren Sin na ganin cewa, yankin tekun Asiya da Fasifik, zai samu ci gaba mai ɗorewa ne kaɗai, idan an gudanar da haɗin gwiwa, tsakanin ƙasashen shiyyar, maimakon haɗa wani gungu na ƙawance, domin yin fito na fito.

Ko shakka babu, lokaci zai ƙara fayyace cewa, duk wasu dabaru da ake gudanarwa domin cimma moriyar ƙashin kai, da nuna wariya, ba za su haifar da ɗa mai ido ba. Kaza lika mafi yawan ƙasashe dake yankin Asiya da Fasifik, za su ci gaba da samun ikon faɗa a ji a nan gaba, a wannan yanki ƙarƙashin manufar zaman tare a gida guda.