Sin ta tallafa wa shirin Covax da Dala miliyan 100

By CRI HAUSA

A yau Litinin 14 ga watan Fabarairu ne, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya shaida wa taron manema labarai cewa, ƙasar Sin ta cika alƙawarin da ta ɗauka, inda a ranar Juma’a 11 ga wata, ta gabatarwa shirin samar da rigakafi na COVAX da gudummawar dalar Amurka miliyan 100, kuɗaɗen da za a yi amfani da su wajen rarraba rigakafin annobar COVID-19 ga ƙasashe masu tasowa.

Wang Wenbin, ya ce tun a yayin taron ƙasa da ƙasa game da haɗin gwiwar samar da rigakafi da ya gabata, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya alƙawarta wannan tallafi. Kuma kamar yadda aka gani a yanzu, Sin ta cika wannan alƙawari yadda ya kamata.

Da aka yi masa tambaya game da matsayin kadarorin babban bankin ƙasar Afghanistan da aka daskarar kuwa, Wang ya ce kadarorin da darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 7, waɗanda aka riƙe a matsayin diyyar harin ta’addanci na ran 11 ga watan 9 na shekarar 2001 da ya auku a birnin New York na Amurka, kadarori ne na al’ummar ƙasar Afghanistan, don haka ya kamata a mayar wa ‘yan ƙasar haƙƙin su, domin su samu damar inganta rayuwa.

Da ya taɓo batun gasar Olympics ta hunturu da birnin Beijing ke karɓar baƙunci yanzu haka kuwa, Wang Wenbin ya ce gasar ta samu tagomashi, inda ake nuna ta ta kafofin talabijin masu matuƙar inganci. Kuma duk da yake ana ci gaba da fuskantar yaɗuwar annobar COVID-19 a sassan duniya, hakan bai karya lagon gasar ba, inda take ci gaba da gudana cikin yanayi na nishaɗantarwa, da bunkasa abota, ƙarƙashin wasannin ƙanƙara da na dusar ƙanƙara dake gudana tsakanin al’ummun sassan ƙasashen duniya masu yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *