MOPPAN ta kama hanyar magance rikicin Kannywood

Daga BASHIR ISAH

A yayin da ake ci gaba da tafka zazzafar muhawara, Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta MOPPAN ta bayyana cewa, ta miƙe domin ɗaukar matakin daƙile rikicin da ya kunno kai a masana’antar Kannywood tun bayan da jaruma Ladin Cima ta bayyana cewa abin da ake biyan ta a masana’antar bai taka kara ya karya ba yayin wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da ita.

A bayyane yake cewa har ila yau, zancen na ci gaba da jan hankalin al’umma, musamman mabiya lamurran fina-finan Hausa, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa dangane da batun. Lamarin da ya sa wasu masu ruwa da tsaki suka fara kiraye-kiraye ga shugabannin MOPPAN da su shiga su magance mahawarar, kamar dai yadda MOPPAN ɗin ta bayyana cikin sanarwar manema labarai da ta fitar ta hannun kakakinta na ƙasa, Al-Amin Ciroma, a ranar Litinin.

Ciroma ya ce, “Sanin mahimmancin kiraye-kirayen ne ya sa MOPPAN, a ƙarƙashin jagorancin Shugabanta na Kasa Dr. Ahmad Muhammad Sarari, ta ke tabbatar wa al’umma, ciki, har da waɗanda suka aika da buɗaɗɗun wasiƙu ga ƙungiyar MOPPAN, cewar ta ɗauki ƙwararan matakai, da haɗin gwiwar sauran ƙungiyoyi, kamar ƙungiyar masu shirin fim ta Arewa, wato AFMAN don shawo kan lamarin.

“Kaɗan daga cikin matakan su ne, MOPPAN ta jawo hankalin dukkanin ɓangarorin da su dakata da musayar yawu, kuma sun dakatar.

“Haka kuma, MOPPAN za ta cimma matsaya ta musamman kan lamarin, bayan shirye-shirye da dama da ta gudanar.”

A ƙarshe, shugabannin ƙungiyoyin sun jaddada kira ga dukkanin ‘ya’yan Kannywood da su kasance masu kishin masana’antar, su kuma daina bin son zuciya wanda ka iya haifra da manyan matsaloli ga sana’ar fim baki ɗaya.