Kasuwanci

NNPC da Ɗangote sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa gas don takin zamani

NNPC da Ɗangote sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa gas don takin zamani

Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin rarraba man fetur na Nijeriya, NNPC, ta bayyana cewa, ta ƙulla yarjejeniya tare da kamfanin attajiri Ɗangote don ta dinga samar musu da gas.  Kamfanin NNPC, ya bayyana cewa, ɓangarorin biyu sun rattaba hannu a yarjejeniyar ne  A garin Abuja yayin taron a kan harkar makamashi na ƙasa karo na biyar. Wanda aka gudanar ranar Alhamis 3 ga watan Maris, 2022. Ɓangarorin da suka qulla yarjejeniya a tsakaninsu sun haɗa da, NNPC, Kamfanin Shell (SPDC), Kamfanin Gas na Total(GACN). Da ya ke faɗar albarkacin bakinsa game da  yarjejeniyar, Mele Kyari, shugaban Kamfanin NNPC ya bayyana…
Read More
Ƙungiya ta nuna qin amincewa da ƙudirin majalisa na gabatar da kadarorin iyalan ma’aikatan banki

Ƙungiya ta nuna qin amincewa da ƙudirin majalisa na gabatar da kadarorin iyalan ma’aikatan banki

Daga AMINA YUSUF ALI Wani sabon ƙuduri da 'yan majalisa suka shigar a  kan ma'aikatan banki a Nijeriya na sanya dokar dukkan ma'aikatan Banki su bayyana kadarorinsu da na mata ko mijinsu da kuma na 'ya'yansu. Ƙungiyar akawu (Ma'aikatan banki) ta Nijeriya ita kuma a nata ɓangaren, ta bayyana tsananin ƙin jininta a kan wannan sabuwar doka da ake son tabbatarwa a Nijeriya. Wacce ta tilasta wa duk wani ma'aikacin/ma'aikaciyar banki su gabatar da dukkan kadarorin da iyalansu suka mallaka.  Kuma a halin da ake ciki har hukumar nan ta yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin…
Read More
Ɗangote ya zarce mamallakin Chelsea a arziki

Ɗangote ya zarce mamallakin Chelsea a arziki

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai, mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Ɗangote, ya sake shillawa sama a cikin jerin sunayen mutanen da suka fi kowa arziki a Duniya. Domin kuwa rahotanni sun bayyana cewa, a yanzu haka ma sunan Ɗangote yana saman sunan Biloniyan attajirin nan na ƙasar Rasha, Roman Abramovich. Kuma mamallakin kamfanin ƙwallon ƙafa na Chelsea. Jaridar Bloomberg ta rawaito cewa, a  yanzu haka ƙarfin arzikin attajirin kuma biloniya, Aliko Dangote ya ƙara haɓaka da ƙarin, Dalar Amurka $934 abinda ya kai shi ga zama mutum na 83 ma fi arziki a…
Read More
Rikicin Ukraine: Fesbuk ya haramta wa Rasha tallata kasuwanci a shafinsa

Rikicin Ukraine: Fesbuk ya haramta wa Rasha tallata kasuwanci a shafinsa

Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin sadarwa na yanar gizo na Fesbuk wanda a yanzu ya rikiɗe ya koma Meta ya haramta wa ƙasar Rasha tallata kasuwanci a shafukansa. Wato dai dukkan kafafen yaɗa labarai mallakin ƙasar, kamfanin ya hana su tallata komai a dandalin na sada zumunta (Fesbuk). A yanzu haka ma dai Kamfanin na Fesbuk wanda aka fi sani da Meta ya dakatar shafukan wasu manyan kafofin yaɗa labarai mallakin ƙasar ta Rasha guda huɗu.  Wannan jawabi na haramci ga ƙasar Rasha ya fito ne daga shafin Tiwita na shugaban sashen tsaro na kamfanin Meta (Fesbuk), Nathaniel Gleicher. Inda…
Read More
Osinbajo da Sanwo-Olu sun ƙaddamar da kamfanonin ƙunzugun jarirai da audugar mata

Osinbajo da Sanwo-Olu sun ƙaddamar da kamfanonin ƙunzugun jarirai da audugar mata

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Juma'ar da ta gabata ne, Mataimakin Shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu suka ƙaddamar da buɗe kamfanonin ƙunzugun mata da jarirai wanda aka yi a kan Dalar Amurka Miliyan $100. Wato sun ƙaddamar da  ƙunzugun jarirai na babban kamfanin Huggies, sannan kuma audugar mata ta kamfanin Kotqex, waɗanda aka gudanar a yankin Odogunyan dake Ikorodu, a jihar Legas. Sabon kamfanin wanda kamfanin Kimberly-Clark Nigeria, a filoti mai faɗin, 86,000m², an fara shi ne a cikin watanni 4 na ƙarshen shekarar da ta gabata, 2021. Amma matsalar dokar annobar…
Read More
Birtaniya za ta ba wa Nijeriya Fam miliyan 10 don bunƙasa makamashi

Birtaniya za ta ba wa Nijeriya Fam miliyan 10 don bunƙasa makamashi

Daga AMINA YUSUF ALI Birtaniya ta yi alƙawarin bayar da Fam Miliyan ɗari ga sashen samar da makamashin Nijeriya. Ministan ƙasar Birtaniya a kan harkokin Afirka, Vicky Ford, ita ta ba da wannan sanarwar a ranar Litinin ɗin da ta gabata. Inda ta bayyana cewa, ƙasar Birtaniyan za ta ba wa Nijeriya tallafin Fam Miliyan 10 don bunƙasa harkar makamashi.  A cewar Malama Vicky Ford, ƙasar tasu za ta ba da tallafin ne ga Nijeriya domin bunƙasar sashen makamashi na ƙasar don samar da sauƙi a kan fanshon ma'aikatan sashen da sauran al'amuran tafiyar da harkar bunƙasa makamashi a Nijeriya.…
Read More
Jarin da Sin ta zuba a fannin binciken kimiyya zai iya kaiwa kusan Yuan tiriliyan 2.79 a shekarar 2021

Jarin da Sin ta zuba a fannin binciken kimiyya zai iya kaiwa kusan Yuan tiriliyan 2.79 a shekarar 2021

Daga CRI HAUSA Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar ƙasar Sin ya gudanar da taron ’yan jaridu a yau, inda ya gabatar da ci gaban da aka samu a fannonin kimiyya da fasahar ƙirƙire-ƙirƙire na ƙasar. Game da jimillar ci gaban da fannin ayyukan kimiyya da fasaha na ƙasar Sin ya samu a shekarar 2021, an gabatar a wajen taron cewa, jimillar jarin da aka zuba a fannin bincike da bunƙasa ci gaban kimiyya da fasaha, ya kai RMB Yuan triliyan 2.79, wato an samu ƙarin kashi 14.2 bisa 100, sama da na shekarar 2020, kuma jimillar alƙaluman jarin da…
Read More
‘Yan kasuwa sun fusata da sabuwar dokar CBN kan sufuri

‘Yan kasuwa sun fusata da sabuwar dokar CBN kan sufuri

Daga AMINA YUSUF ALI ’Yan kasuwa masu shigo da kaya daga ƙasashen waje zuwa Nijeriya sun caccaki sabuwar dokar Babban Bankin Nijeriya (CBN) a kan harkar fatauci. Sannan kuma sun gargaɗi al'umma a kan hauhawar farashi da tsadar rayuwar ma gabaɗaya.  'Yan kasuwar sun nuna tsananin ɓacin ransu game da dokar da CBN ta kafa a kan tilas kowanne ɗan kasuwa mai shigo da kayan ƙasar waje ya yi rajista a zauren yanar gizo na CBN ɗin, sannan kuma tilas ya amince da tsarin daidaita farashi da Bankin ya tsara.  A kan haka 'yan kasuwar suke gargaɗin al'umma da su…
Read More
Kamfanonin jiragen sama na waje za su ƙwace harkar sufuri a Nijeriya – ’Yan Majalisa

Kamfanonin jiragen sama na waje za su ƙwace harkar sufuri a Nijeriya – ’Yan Majalisa

Daga AMINA YUSUF ALI Haɗaɗɗen kwamitin majalisar dokokin tarayya a kan harkar sufurin jirgin sama ta bayyana cewa, nan da wani lokaci kaɗan, kamfanonin sufurin ƙasar waje za su ƙwace harkar sufurin jirgin sama in dai har na Nijeriya ba su gyara kura-kuran da suke da su ba.  Babbar matsalar da kwamitin ya ja kunnen kamfanonin sufurin jirgin saman Nijeriya ita ce, ba sa iya gudanar da harkar tashi ko saukar jirage ba tare da saɓa lokaci ba. Idan kuwa wannan matsalar ta cigaba a cewar su, to hakan zai ba wa kamfanonin sufurin na ƙasashen waje damar ƙwace harkar…
Read More
Dokar hana ci da safarar jakai babbar illa ce gare mu, cewar dilolin jakai

Dokar hana ci da safarar jakai babbar illa ce gare mu, cewar dilolin jakai

Daga AMINA YUSUF ALI Diloli masu safarar jakuna a faɗin Nijeriya sun koka matuƙa a kan dokar da gwamnatin tarayya ta riga ta zartar a kan hana ci da safarar jakunan.  Shugaban ƙugiyar dilolin jakuna ta Nijeriya, Mista Dike Ifeanyi shi ya bayyana haka a yayin zantawar sa da manema labarai a game da dokar hana safara da cin jakunan da sayar da abinda ya shafe su da gwamnatin Nijeriya ta sanya a 'yan kwanankin nan. Inda ya bayyana wasu daga cikin alfanun kiwatawa da cinikin jakunan a ƙasar nan.  Daga cikin falalar jakunan a cewar sa, sun haɗa da,…
Read More