Kamfanonin jiragen sama na waje za su ƙwace harkar sufuri a Nijeriya – ’Yan Majalisa

Daga AMINA YUSUF ALI

Haɗaɗɗen kwamitin majalisar dokokin tarayya a kan harkar sufurin jirgin sama ta bayyana cewa, nan da wani lokaci kaɗan, kamfanonin sufurin ƙasar waje za su ƙwace harkar sufurin jirgin sama in dai har na Nijeriya ba su gyara kura-kuran da suke da su ba. 

Babbar matsalar da kwamitin ya ja kunnen kamfanonin sufurin jirgin saman Nijeriya ita ce, ba sa iya gudanar da harkar tashi ko saukar jirage ba tare da saɓa lokaci ba. Idan kuwa wannan matsalar ta cigaba a cewar su, to hakan zai ba wa kamfanonin sufurin na ƙasashen waje damar ƙwace harkar sufurin kamfanonin gida kuma su cigaba da jan ragamarsu a harkar. 

Waɗannan bayanai suna ƙunshe ne a cikin jawabin da Sanata  Smart Adeyemi da ɗan Majalisar wakilai, Nnolim Nnaj. An gabatar da jawabin ne a yayin taron ganawar da ‘yan Majalisar Dattawa da kwamitin majalisar a kan harkar sufurin jirgin sama,  da kuma Hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta Nijeriya (NCAA) wanda aka gudanar ranar Juma’ar da ta gabata, a jihar Legas. 

Adeyemi ya qara da cewa, manufar taron ganawar shi ne, don a yi ga wuri ga waina. Wato a ji matsalolin da sashen sufurin yake fuskanta daga bakin waɗanda abin ya shafa.

A cewar sa, ‘yan Nijeriya suna matuqar baƙinciki da Allawadai da abubuwan da suke faruwa. Shi ya sa Kwamitin nasu yake buƙatar amsoshi don samo bakin zare.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, kamfanonin sufufin na gida Nijeriya sun riga sun saba da rashin kyautatawa ga fasinjoji. Inda wasu lokutan sukan soke ko su saɓa lokacin tashi ko saukar jiragen. Inda za a samu jinkirin awanni 5 ko shida  ba tare da sun ba wa fasinjoji haƙuri ko fansa a kan haka ba. A cewar sa, banda matsalar tsaron ƙasar nan, mutane sun gwammace su yi tafiyarsu a mota. 

A shekarar 2018 sakamakon rahotanni sun bayyana cewa,  fiye da kashi 60 na  lokutan jirgin sama an soke su ba bisa ƙa’ida ba. Haka a shekarar da ta gabata ta 2021, an rawaito kamfanonin sufuri na Azman da Airpeace sun jinkirta fiye da kaso 50 na lokutan tashin jiragensu.