‘Yan sanda sun ceto mata bakwai da kashe ɗan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar fatattakar wasu ‘yan bindiga tare da ƙwato mata 4 da ƙananan yaransu guda 3 a ƙauyen Gandun Ƙarfi dake cikin ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Kakakin rundunar  SP Gambo Isa ne ya bayyana hakan jiya alhamis 17 ga Fabarairu, 2022 a wani taron manema labarai da rundunar ta kira don sanar da al’umma yadda jami’an ‘yan sanda ke ƙoƙarin yaƙar ‘yan ta’adda da suka addabi wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar.

SP Isa ya bayyana cewar ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun afkawa ƙauyen Gandun Ƙarfi a Larabar makon jiya, inda bayan sun firgita mazauna garin da harbe-harbe suka kuma sace mata 7 ciki har da qananan yara.

“Mun samu gagarumar nasara a jiya inda ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai akan babura sun farwa ƙauyen Gandun Ƙarfi suka sace mata 4 da yayansu guda 3,” inji shi.

SP Isa ya ƙara da cewa bayan samun bayanan sirri da su ka yi dake nuna cewar ‘yan bindigar sun bi ta hanyar ƙanƙara rundunar ba ta yi wata-wata ba ta sanar da DPO na ƙaramar hukumar Ƙanƙara inda ya tunkari ‘yan ta’addar don hana su nufa daji da matan da suka sato.

Jami’an ‘yan sandar sun yi musayar wuta da ɓarayin a hanyar Ƙanƙara zuwa Sheme a wani ƙauye da ake kira Zurunkutum, inda suka samu nasarar hallaka ɗaya daga cikin ‘yan bindigar tare da ƙwato bindiga ƙirar AK47 gami da harsasai a hannunsa.

Bayan haka rundunar ta ƙwato dabbobi 152 da suka haɗa da shanu 82 da kuma tumaki 70 daga wajen su.

Haka zalika kakakin rundunar ya bayyana cewar sun sake samun wata nasarar a ranar Talata inda suka fatattaki wasu ɓarayin daji da suka addabi hanyar Zango zuwa Qanqara tare da kashe ɗaya daga cikin su.

“Ɓarayin sun addabi wata ƙaramar hanya inda suke tare mutanen gari da kuma ‘yan kasuwa suna ƙwace masu dukiyoyi sai dai bayan musayar wuta DPL na ƙaramar hukumar Ƙanƙara ya yi nasarar kashe ɗaya daga cikin su tare da ƙwato babur qirar Boxer daga wajen su,” inji SP Isa.

Daga ƙarshe kakakin rundunar ya ce su na ci gaba da bincike akan lamarin.