‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 4 a Neja

Daga BASHIR ISAH

Wasu ‘yan bindiga sun halaka jami’an ‘Civil Deffence’ huɗu tare da ƙona wasu mutanen da ba tantance adadinsu ba ƙurmus a ƙauyen Galadiman Kogo da ke yankin ƙaramar hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Shaidu sun ce haka waɗannan mutanen da aka cinna ma wuta suka ƙone ƙurmus ba tare da samun agaji ta kowane ɓangare ba, don kuwa duk wanda ya leƙo waje a wannan lokacin ‘yan bindigar za su harbe shi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, Mr Monday Kuryas ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce jami’an tsaron NSCDC su huɗu tare da wasu mazauna yankin su shida ne suka rasa rayukansu a harin.

Ya ƙara da cewa, jami’an tsaron sun taka wata nakiya ce da ‘yan bindigar suka ɗana yayin da suke wucewa a motarsu a yankin wanda hakan ya yi ajalin wasu daga cikinsu.

Ya ce da sanyin safiyar Litinin ne ‘yan bindigar suka far wa ƙauyen inda suka banka wa gidaje takwas wuta har da ginin da jam’ian tsaron haɗin gwiwar da aka tura yankin suke da zama.

Shi ma Shugaban Ƙaramar Hukumar Shiroro, Mr Suleiman Chukuba ya tabbatar da faruwar harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *