Kasuwanci

Kwastom ta cafke motar ‘yan sanda da ake shigo da shinkafa da ita

Kwastom ta cafke motar ‘yan sanda da ake shigo da shinkafa da ita

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar hana fasa-ƙwauri (Kwastom) dake kula da shiyar jihar Ogun ta kama motar ‘yan sanda maƙare da shinkafar gwamnati. Shugaban hukumar Kwastom Shiyyar Jihar Ogun, Bamidele Makinde ya sanar da haka ranar Talata da ta gabata yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Abeokuta. Makinde ya ce, motar da hukumar ta kama ƙirar ‘Hilux van’ na xauke da lambar PF 10889 SPY sannan an loda ta da manyan buhunan shinkafa 2,750. Ya ce direban dake tuka motan dai ya gudu. Makinde ya ce, duk da an ga motar da lambar motar ‘yan sanda da…
Read More
Rikicin Yukren: Rasha ta amince da amsar Bitkoyin a matsayin kuɗin cinikin gas

Rikicin Yukren: Rasha ta amince da amsar Bitkoyin a matsayin kuɗin cinikin gas

Daga AMINA YUSUF ALI Ƙasar Rasha ta ba da dama ga masu sayen gas a wajenta da za su iya biya da kuɗaɗen ƙasar da suka ga dama ko ma bitkoyin. Shugaban kwamitin ƙasar Rasha a kan harkar makamashi shi ya bayyana haka. Amma fa ba kowacce ƙasa za a iya yin wannan ciniki da ita ba, sai ƙasashen da suke 'ɗasawa' da ƙasar ta Rasha.  Mujallar Ingilishi wacce take labarai a kan Bitkoyin, Namcios  Bitcoin Magazine ta rawaito cewa, Shugaban Kwamitin na makamashi a ƙasar Rasha mai suna Pavel Zavalny, ya bayyana cewa, ƙasar Rasha za ta fara amsar…
Read More
Ba ma’aikacinmu da ya rasa ransa a gobarar kamfanin simintin BUA a Sakkwato – BUA

Ba ma’aikacinmu da ya rasa ransa a gobarar kamfanin simintin BUA a Sakkwato – BUA

Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin Samar da Siminti na BUA dake Sakkwato ya bayyana cewa, mutum uku da suka mutu a sanadiyar gobarar da ta tashi a masana’antar Simintin BUA a Sakkwato, ba ma’aikatan kamfanin ba ne, ‘yan ina-da-aiki ne. Wannan bayani yana ƙunshe ne a wata sanarwa da Sada Sulaiman, Daraktan Gudanarwa na BUA Cement ya aiko wa Jaridar PREMIUM TIMES. Ya qara da cewa,  waɗanda tsautsayin ya ritsa da su, suna aiki ne a ƙarƙashin wani mai aikin kula da gyare-gyare na lafiyar inji. A kwanakin baya da ma jaridar ta buga labarin yadda wuta ta tashi a…
Read More
Majalisa tana bibiyar kamfanonin mai 77 kan rashin biyan haraji

Majalisa tana bibiyar kamfanonin mai 77 kan rashin biyan haraji

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Talatar da ta gabata ne dai majalisar Wakilan Nijeriya ta cigaba da sauraron wani jawabi a game da bincike game da bashin Naira Tiriliyan 2.6tn da gwamanatin tarayya take bin kamfanonin mai guda 77 a Nijeriya.  Majalisar tana gudanar da wannan bin diddigi ne da dogaro da rahoton da aka samar a kan kamfanonin da suka shafi albarkatun ƙasa a shekarar 2019. Kakakin Majalisar Wakilan, Femi Gbajabiamila ya yi barazanar cewa, in dai kamfanonin da ake bin bashin ba za su ba da haɗin kai ba, to kuwa za su tilasta wa majalisar ɗaukan…
Read More
Ali Nuhu ya zama jakadan wani kamfani a Arewacin Najeriya

Ali Nuhu ya zama jakadan wani kamfani a Arewacin Najeriya

Daga AMINA YUSUF ALI An naɗa fitaccen jarumin finafinan Hausa na Kannywood, Ali Nuhu, a matsayin jakadan kamfanin Checkers Custard na Arewacin Najeriya. Jaridar yanar gizo ta Labarai24.com ta rawaito cewa, an yi naɗin ne a wani taro da kamfanin Checkers Africa suka shirya a jihar Kano da ke Arewa maso yammacin ƙasar. A cewar babban Manajan Kamfanin Checkers da ke nahiyar Afirka, Mista Karan Checker ya bayyana cewa, la’akari da irin shaharar da jarumin ya yi a masana’antar Kanywood da arewacin Najeriya ya sanya kamfanin na Checker ya naɗa shi a matsayin jakadansu na shiyyar Arewa. A yayin  da ya…
Read More
Ƙarancin lantarki: Wasu kamfanoni sun yanke shawarar ficewa daga Nijeriya

Ƙarancin lantarki: Wasu kamfanoni sun yanke shawarar ficewa daga Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Fiye da makonni uku kenan a ke fama da matsalar ƙarancin wutar lantarki da fetur a Nijeriya, abunda ƙarara ya jefa al’umma cikin mawuyacin hali. Yanzu haka dai kamfanoni da dama sun dakatar da ayyukansu, yayin da wasu kuma ke shirin ƙaura zuwa maƙwabtan ƙasashe.To ko yaya girman matsalar take a masana’antun jihar Kano?  Gidan Rediyon rfi ya rawaito a shafinsa na yanar gizo cewa, wani Kamfanin sarrafa auduga a jihar Kano mai suna Amarya Cotton sun yanke shawarar za su tattara komatsensu su koma ƙasar Chadi domin cigaba da harkar kasuwancinsu.  Shugaban Kamfanin Amarya Cotton…
Read More
Attajirin Saudiyya ya taya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea kan Yuro Biliyan 2.7

Attajirin Saudiyya ya taya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea kan Yuro Biliyan 2.7

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da ƙasar Ingila take tsaka da ɗaukar matakan ladabtarwa ga attajirin biloniyan nan ɗan ƙasar Rasha, Roman Abramovich kuma ƙungiyar ƙwallo ta Chelsea, wacce mallakinsa ce ta shiga cikin halan-halahu. Wato gwamnatin ƙasar ta saka shi a kasuwa tana so ta sayar da shi nan ba da daɗewa ba. Kodayake, a kwanankin baya da attajirin ya yi niyyar sayar da shi, an ji gwamnatin ta tsayar da tallan ƙungiyar a yayin da take gabatar da matakan ladabtarwa ga shi Abramovich ɗin. Amma a halin yanzu ana tsammanin gwamnatin ta shirya tsaf, don cefanar da…
Read More
Tsada da ƙarancin fetur: Mun kusa rufe harkar sufuri – Kamfanonin jiragen sama

Tsada da ƙarancin fetur: Mun kusa rufe harkar sufuri – Kamfanonin jiragen sama

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na Nijeriya sun bayar da sanarwar yiwuwar su rufe harkokinsu na sufuri nan da kwanaki kaɗan masu zuwa. Kasancewar abokin aikin nasu na sufuri wato man fetur ya yi tsananin ƙaranci kuma farashinsa ya ƙara hauhawar fiye da ƙima. Wato ana sayar da shi a kan farashin Naira 600 kowacce lita guda.  Allen Onyema, babban jami'in zartarwa na kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Airpeace shi ya bayyana haka a yayin da yake magana da yawun sauran kamfanonin jiragen saman. Ya bayyana haka a yayin da yake jawabi a…
Read More
Attajirin da ke neman wuce Ɗangote a Afrika ya tafka mummunar asara

Attajirin da ke neman wuce Ɗangote a Afrika ya tafka mummunar asara

Daga AMINA YUSUF ALI Biloniya, Johann Rupert wanda ya yi ƙaurin suna wajen takara da ganin ya wuce Alhaji Aliko Ɗangote kuma ya maye gurbinsa a matsayin mutum mafi arziki a Afirka ya tafka asarar Dalar Amurka kusan ɗaya da rabi a cikin ƙasa da mako guda.  Jaridar Ingilishi ta Bloomberg ta rawaito cewa, Johann Rupert ɗin wanda asalinsa xan Afirka ta kudu ne, kuma wanda ya jima yana hararar kujerar Ɗangote ta mutumin da ya fi kowa arziki a Duniya. Ya tafka asarar, Dala biliyan ɗaya da kusan rabi a cikin kwana biyar kacal.   Rahotanni sun bayyana cewa, tun…
Read More
Aikin tashar sauke kayan teku a Kano ya kai kashi 80%

Aikin tashar sauke kayan teku a Kano ya kai kashi 80%

Daga WAKILINMU A halin da ake ciki, aikin tashar sauke kayan teku da ke Kano, wanda Gwamnatin Shugaba Buhari ke gudanarwa ya kai kashi 80 cikin 100 da kammaluwa. Bayanin hakan ya fito ne daga tawagar duba aikin a ƙarƙashin jagorancin Ministan Sufuri, Rt. Hon. Rotimin Amaechi, ranar Asabar, 5 ga Maris, 2022, inda tawagar ta jaddada cewa wannan tashar mai suna Dala za a sanya a jerin matsayi irin na kowacce tashar jirgin ruwa, idan an kammala ta. Gina wannan tashar zai dawo da martabar Kano a matsayin Babbar Cibiyar Kasuwanci a Arewa da ma Yankin Afrika ta Yamma…
Read More