26
Apr
Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar tattara haraji ta tarayyar Nijeriya, FIRS, ta miƙa kambun girmamawa ga Jihar Yobe a matsayin jihar da ta fi kowacce jiha tattara haraji mai yawa daga cikin jihohi na shirya ta 'B'. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya rawaito. Jihar Yobe ita ce ta lashe gasar FIRS a matsayin jahar da ta yi zarar a samar da haraji ga hukumar daga jihohin shiyyar 'B'. Shugaban tsare-tsaren FIRS na shiyyar B, Mista Mohammed Mayanda, shi ya bayyana haka a ranar Juma'ar da ta gabata a garin Damaturu, jim kaɗan bayan ya miƙa kambun girmamawar…
