FIRS ta karrama Yobe saboda lashe gasar jiha mafi tara mata haraji a 2021

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar tattara haraji ta tarayyar Nijeriya, FIRS, ta miƙa kambun girmamawa ga Jihar Yobe a matsayin jihar da ta fi kowacce jiha tattara haraji mai yawa daga cikin jihohi na shirya ta ‘B’. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya rawaito. 

Jihar Yobe ita ce ta lashe gasar FIRS a matsayin  jahar da ta yi zarar a samar da haraji ga hukumar daga jihohin shiyyar ‘B’. 

Shugaban tsare-tsaren FIRS na shiyyar B, Mista Mohammed Mayanda, shi ya bayyana haka a ranar Juma’ar da ta gabata a garin Damaturu, jim kaɗan bayan ya miƙa kambun girmamawar ga gwamnan jihar, Mai Mala Buni.

Jihohin da suke ƙunshe  a shiyyar ta ‘B’ su ne, Yobe, Borno da kuma Bauchi.

Mayanda ya bayyana cewa, Yobe ta taka rawar gani wajen tattara ɗimbin haraji mai yawa da fatan sauran jihohin da suke a shiyyar za su yi koyi da irin jajircewarta a tattara haraji ba tare da sanya ba. 

Da yake jawabi bayan amsar kambun girmamawar, Gwamna Buni na jihar Yobe ya ƙara jaddada cewa, jihar tasa za ta cigaba da ƙoƙarin ta kamar yadda gwamnatin Tarayya ta yaba mata domin ƙara kyautata alaƙarta da gwamnatin Tarayyar.