’Yan Nijeriya Miliyan 33.4 na amfani da Kirifto Karansi duk da haramcin CBN – Bincike

Daga AMINA YUSUF ALI 

Rahotanni sun nuna cewa, kaso 20 da shiga daga masu zuba hannun jari a harkar sulalla na yanar gizo da aka fi sani da Kirifto Karansi sun fara dillancinsa a kwanakin nan.

Haka zalika sabon rahotan ya bayyana cewa kaso 35 na balagaggun mutanen Nijeriya suna zuba hannun jari a kasuwancin sulallan. 

Kodayake a kwanakin nan Babban Bankin Nijeriya ya haramta amfani ko hada-hadar sulallan Kirifto karanci a dukkan bankunan Nijeriya. Amma duk da haka, rahotanni sun bayyana cewa, kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 33.4 sun mallaki kadara ta Kirifto ɗin ko kuma suna hada-hadar cinikayyarsa. 

Haka nan kuma wata majiya mai alaƙa da sana’ar Kirifto ɗin ta bayyana cewa, kasuwar Kirifto cike take da mutane ‘yan shekaru 18 zuwa shekaru 60.

Haka a wani sakamakon bincike da zauren  ‘Google’ ya yi a farkon shekara ta 2021 an bayyana cewa, Nijeriya ita ce ƙasar da ta fi kowacce neman bayani a game da Kirifto a zauren Google ɗin, kuma kullum qara ƙaruwa masu hada-hadar sa suke yi a ƙasar. 

Haka zalika, binciken ya ƙara bayyana cewa, matasan Nijeriya su ne ummul’aba’isin na haɓakar yawan masu amfani da Kirifto Karansi a Duniya. Sannan kuma sakamakon binciken da aka yi a na kwana-kwanan nan a farkon shekarar nan ta 2022 ya nuna cewa, kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 3.4 wato kaso 35 na masu shekaru 18 zuwa 60 ne suka mallaka ko kuma suke hada-hadar Kirifto a watanni shida baya. Kuma a cewar rahoton har yanzu akwai masu sha’awar shiga, akwai kuma masu hada-hadar da suke son ƙara bunƙasawa. Shi ya sa a cewar su kullum harkar take ƙara bunƙasa a Nijeriya.

Amma a ra’ayin ‘yan canjin Kirifto suna ganin faɗuwar warwas da Naira ta yi ne da kuma tsadar rayuwa da tattalin arziki ga annobar Korona a Nijeriya su suka jawo ‘yan Nijeriya suka rungumi harkar Kirifto Karanci a matsayin mafita. Wadda mutane da dama a ƙasar suka fara harkar ta Bitkoyin tun shekaru shida da suka shuɗe. Kuma har yanzu suna kan bakansu duk kuwa da sanarwar da CBN ya yi na cewa ya haramta harkar.