Mace ’yar kwalliya ce

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake saduwa a cikin shafin kwalliya na jaridar al’umma Manhaja. Allah ya karɓi ibadunmu Ya sa mu cikin bayinSa da zai ‘yanta a wannan wata na Ramdana. 

A halittar ‘ya mace a duk inda ta tunkaro, ana fara kallon abin da ta sa, yanayin shigar ta kafin kallon halittar jikinta. Wannan na nufin shigar mace ko kwalliyar ta ce annurinta. Duk kyawon ki, zai samu nakasu inhar ba kya gyara ko ince kwalliya.

Kwalliyar da na ke magana kai a nan ba wai ta shafe-shafen kayan ƙyalƙyali ko ƙarin haske ko canza wani fasali na jikinki ba. Ko amfani da wasu ababe na bugi don ƙara wa wata halitta taki girma ko kyan gani ba.

Duk waɗannan da na zayyano illa ce gare ki ya ke ‘yar uwa mace, domin za ki more su ne na ɗan wani lokaci ne, yayin da za su yi ma ki illar da ta fi amfaninsu yawa.

Ina magana ne kan gyara da ita fata ta aminta da shi, wanda zai sa ta haske da ƙyali ba tare da ya cutar da ita ba. Ina magana kan sanin yadda za ki damu da duk wani baƙon abu da ya riske fatarki tare da sanin sahihiyar hanyar kawar da shi.

Ya ke mace, ki sani, babu matsala ta fata ko gyaran fata da ba za ki samu mafitar sa ba ta hanyar amfani da ababe marar cutar wa ba. Musamman ma a tsakanin tsiro da Allah ya wadata mu da su. Abin da kawai kike nema shine, sanin abin da ya dace da ta ki matsala. Misali;

Idan kina fama da matsalar koɗewar fuska wadda yawan shiga rana ya haifar, ta inda za ki ga fatar fuskarki ta za ma kala biyu ko kuma ta ƙone, to za ki iya amfani da aloe bera don magance matsalar.

Yadda za ki yi amfani da ita kuwa mai sauƙi ne. Ki daka ko ki matse ruwan ta, sai ki haɗa da ruwan lemon tsami kaɗan, ana shafa wa a fuskar, mintuna kaɗan sai a wanke. Da yardar Allah za ki nemi wannan matsalar ki rasa.

Misali na biyu; gautsin fata, mai fama da wannan zai iya haɗa gurji da markaɗaɗɗen dabino tare da ruwan aloe vera, ya dinga shafe fatar da haɗin tsayin minti 45, sannan a wanke.

Kai ko da gashinki ne damuwarki, za ki iya magance matsalar zubewar gashin ta hanyar haɗa zuma da zaitun tare da ruwan aloe vera, sai kin tabbatar sun haɗe kafin ki shafe gashin da shi, ki tabbatar tun daga farar kai har saman gashin sun samu.

Sai ki rufe da leda tsayin awa ɗaya kafin a wanke. Maimaita wannan na ƙara wa gashin baƙi da ƙarfin da zai hana shi ci gaba da ƙarewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *