Amfanin dabino a jikin ɗan adam (2)

Daga BILKISU YUSUF ALI

Kamar yadda muka faɗa a makon da ya gabata. Dabino shahararren itaciya ce a duniya da ta shahara. Binciken masana da ƙwararrun masana kiwon lafiya ya tabbatar cewa dabino yana da sinadari masu tarin yawa wanda ke da tasirin gaske wajen bunqasa lafiya da garkuwar jikin ɗan’adam. Dabino yana da sinadarai kamar su magnesium da calcium da potassium da makamantansu. A addinin Musulunci dabino yana da tasiri da gurbi na musamman. Dabino yana da matuƙar amfani a jikin ɗan’adam wanda zai yi wuya a iya zayyano amfaninsa a lokaci guda. Daga cikin amfaninsa akwai:-

Ana sarrafa dabino ta hanyoyo daban-daban ga ma’aurata domin samar musu da zaman lafiya da nutsuwa a zamantakewar auran nasu.

  1. Ga matar da take da matsalar rashin ni’ima take bushewa kuma an tabbatar bat a da sanyi a jikinta to za ta iya yin wannan haɗin na dabino. Ta samu garin dabno da kanunfari in tana da hali ta haɗa da cukwi da ganyen idon zakara kaɗan ta dake shi amma dabinon ya fi yawa a ciki ta samu mazubi me kyau ta adana shi a kullum ta ɗauki babban cokali ɗaya ta zuba a madara me kyau ko nono ta sha safe da kuma yamma. In har za ta dimanci hakan ni’imarta za ta dawo da yardar Allah. Haka mace marar sha’awa duk wannan haɗin zai yi mata magani.
  2. ma’aurata duka su biyun suna iya samun dabino a ƙalla guda goma a sa a madara ko nono su ci ko su markaɗa su sha. Yana da kyau tsakanin ma’aurata.
  3. Haka ga namijin da yake da ƙarancin maniyyi ko kuma yake da rauni shi ma ya samun dabino da dama a gyara shi a samu citta da kanumfari da girfa da namijin goro a dake su ya yi laushi a samu zuma me kyau a cuɗe su a ciki. Ana shan babban cokali safe da yamma sannan kuma ana iya saka wa a madara me ɗimi a sha don a ƙara masa ƙarfi.
  4. Wanda yake da yara waɗanda ba sa fahimtar karatu ana samun dabino a daka shi a haɗa shi da garin na’a-na’a da garin habbatus sauda a cuɗe shi a ke tafasa musu suna sha kamar shayi za su sami fahimta da ma nutsuwa.

5, Ga waɗanda ba su da qarfi ko kwarin ƙashi ana samun dabino a jiqa shi in ya jiƙu a markaɗa shi ya zama juice ake sha in sha Allah za a dace a rashin kwarin ƙashi.

  1. Ga mata da ke son gyaran jiki a gansu jikinsu gwanin sha’awa kuma da kuzari . Sai su sami dabino da kokumba (cucumber) a ke markaɗa su su zama juice a sha a ƙalla kofi ɗaya kullum. Jiki zai yi kyau lafiya za ta inganta ƙananan cutoci duk za su kau da yardar Allah.

Ga mai neman ƙarin bayani ya turo saƙon tes a wannan layin ko ta whatsup: 070 88683334 ko a duba facebook page ɗina Bilkisu Yusuf Ali