Kasuwanci da rashin lokaci suka sa ban mallaki gidan kaina ba – Biloniya Elon Musk

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da manyan attajirai musamman a Nijeriya suke rige-rigen mallakar katafarun gidajen shiga su kwanta, ko su adana a matsayin kadara, Ba’amurken Biloniya nan Elon Musk wanda shi ne mutumin da ya fi kowa kuɗi a Duniya ya bayyana cewa, har yanzu shi ba shi da gidan kansa. 

Attajirin Biloniyan a wani bidiyo da aka yi hira da shi ya bayyana cewa, shi a halin yanzu bai mallaki gidan kansa ba sai dai ya yi ta zaga gidajen abokansa yana kwana. 

Elon Musk ya yi wannan tattaunawar tare da ‘yan jaridu a ranar Litinin a yayin da yake tsaye a kamfanin motocin da naTesta dake Berlin a ƙasar Amurka. Wannan daɗaɗɗiyar hira ce wacce aka yi tun watan Agustan Bara. Kuma kamfanin TED da ya yi hirar shi ya wallafa bidiyo a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

A yayin da yake amsa tambayoyi game da irin tsangwamar da sukar da masu arziki suke fuskanta a wajen mutane, saboda dukiyar da suka mallaka.

Sannan Biloniyan ya bayyana cewa ba shi da jirgin ruwa mai tsada ko wasu wuraren shakatawa don more rayuwa. Abinda ya mallaka dai shi ne jirgin sama nasa na kansa. Shi ma ba domin komai ba sai don ya rage ɓata lokaci wajen gudanar da harkokinsa. 

A halin yanzu dai Musk, yana da ƙarfin arzikin da ya kai Dalar Amurka biliyan $251 billion, kamar yadda jaridar Ingilishi Bloomberg ta rawaito. Inda ya ƙara da cewa, yana matuƙar jin takaicin yadda mutane suke sukar masu kuɗin Duniya. Inda ya buga misali da yadda wata ‘yar majalisar Amurka Sanata Elizabeth Warren, ta soke shi a kan rashin biyan haraji mai yawa. 

Biloniyan ya bayyana cewa, dalilin rashin biyan harajinsa da yawa shi ne, saboda yana taƙaita facaka da dukiyarsa. Sannan kuma harkokin kasuwancinsa su suke cinye masa lokacinsa ba ya samun wata damar morar dukiyarsa yadda ya kamata. Kuma ya sayi jirgin sama ne saboda idan babu shi, lokacin aikinsa na kowacce rana zai ragu.

Wannan ba karamin abin al’ajabi ba ne, yadda mutumin da ya fi kowa arziki a Duniya ba shi da muhalli nasa na kansa. Rahotanni sun bayyana cewa su kansu abokansa suna ƙorafi a kan wannan hali nasa na ƙin yin facaka da dukiyarsa kasancewarsa mai arzikin gaske. Haka ma wata tsohuwar budurwarsa, Vanity Fair ta tava bayyana cewa, akwai lokacin da ta tursasa masa ya sayi sabuwar katifa ya ƙi, duk da tasa ta tsufa har ta yi rami. Ikon Allah, Allah ɗaya har bamban.