Da ɗumi-ɗumi: Jonathan ya amince ya koma APC don takarar Shugaban Ƙasa a 2023 – Reuben Abati

Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Reuben Abati, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, ya shirya tsab domin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Abati ya ƙara da cewa Jonathan zai bayyana aniyyarsa ta takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyya mai mulki, APC nan ba da daɗewa ba.

Da ma dai wasu rahotanni sun nuna tsohon shugaban ƙasar ya gindaya sharaɗin cewa zai koma APC ne idan har za a ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023.

Ko a ranar Asabar wasu magoya bayan Jonathan ɗin sun ziyarce shi a gidansa na Abuja inda suka buƙaci ya fito takarar shugaban ƙasa.

Sai dai, sa’ilin da yake yi wa magoya bayan nasa jawabi, Jonathan ya nuna musu cewa yana aiki a kan wani abu tukuna.

Amma kuma an ga Abati ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tantance cewa Jonathan ya amince ya sauya sheƙa zuwa APC don ba shi damar cika burinsa na neman shugabancin ƙasa.