Buhari ya gama lalata rayuwar ‘yan Nijeriya – Hassan Mathew Kukah

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban limamin mabiya ɗariƙar Katolika da ke Sakkwato, Bishop Mathew Hassan Kukah ya bayyana cewar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kammala lalata duk wani ɓangare na rayuwar jama’ar ƙasar a ƙarƙashin gwamnatin sa tare da bai wa cin hanci da rashawa damar haɓaka.

Yayin da yake gabatar da saƙon bikin Easter a mujami’ar sa, Kukah ya ce duk wani ɓangaren rayuwar jama’ar Nijeriya ya lalace, yayin da ƙasar ta zama sashen gobe da nisa na asibiti ɗauke da tarin marasa lafiya.

Limamin ya ce zukatan ‘yan Nijeriya tare da iyalansu da gidajen su da mujami’u da masallatai da kayan more rayuwa duk sun ruguje a ƙarƙashin gwamnatin Buhari.

Kukah ya ce harkokin ilimin ƙasar ya ruguje tare da rayuwa da makomar ’yan ƙasar kamar yadda ɓangaren siyasa da tattalin arziki da makamashi da al’ummomi da hanyoyin mota da na jiragen ƙasa suka ruguje, inda babu abinda ke rayuwa yadda ake buƙata da ya wuce cin hanci da rashawa.

Limamin ya ce yau ‘yan Nijeriya ba sa iya gane ƙasar su saboda yadda ta fita daga cikin hayyacin ta sakamakon matsalolin da suka mamaye ta a ƙarƙashin gwamnatin Buhari.

Kukah ya ce lura da irin waɗannan ɗimbin matsalolin da suka addabi Nijeriya wasu ‘yan ƙasar na tambayar ko masu riƙe da madafun ikon ba sa ji ko gani ko ɗanɗanar irin yanayin da jama’ar ƙasar suka samu kan su ne ko kuma suna nuna halin ko-in-kula ne domin babu abinda ya dame su.

Limamin ya ce babban ƙalubalen dake gaban jama’ar Nijeriya a yau ita ce yadda za a fara ɗaukar matakin sake dawo da kimar ƙasar da fatar mutane za su rayu har zuwa lokacin zaɓen shekara mai zuwa da kuma sanya ido akan abinda zai biyo baya domin fuskantar matsalolin da suka addabi ƙasar ta hanyar gina halayen jama’a da kuma son ƙasa.

Kukah ya buƙaci shugabannin addinai da su tashi tsaye cikin gaggawa domin ceto Nijeriya daga halin da ta samu kanta, musamman ganin yadda yanzu ake samun miliyoyin mutane a cikin ƙasar da duniya baki ɗaya dake barin addinin Kirista da Musulunci domin zama marasa addinai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *