Wahalar ruwa: Ganduje ya bada umarnin gyara rijiyoyin burtsatsen Birnin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta umarci Hukumar Samar da Ruwan Sha da Tsaftar Muhalli (RUWASSA) da ta gaggauta gyara dukkan rijiyoyin burtsatse da su ka lalace a ƙananan hukumomi takwas na cikin ƙwaryar Birnin Kano, a wani mataki na magance matsalar ruwan sha a jihar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Abba Anwar, Babban Sakataren yaɗa labarai na gwamna Abdullahi Ganduje ya fitar ranar Lahadi a Kano.

Ya ce, Ganduje ya bada umarnin ne a wani taro da jami’an Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta jiha, RUWASSA da kuma shugabannin ƙananan hukumomi takwas na jihar.

Gwamna Ganduje ya samu wakilcin mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf-Gawuna a wajen taron.

Anwar ya ambato Ganduje ya na cewa, “ya kamata RUWASSA ta kuma ɗauki jerin sunaye, musamman a ƙananan hukumomi 44 da ke buƙatar rijiyoyin burtsatse, tare da la’akari da matsalolin da yawaitar rojiyoyin burtsatse ke haifarwa ga muhalli.”

Gwamnan ya kuma umurci kansilolin manyan biranen jihar da su yi amfani da tankunan ruwa don raba ruwa ga mazauna yankunan a wurare masu muhimmanci, a matsayin mafita cikin gaggawa.

Ya kuma bada tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumar raya ƙasar Faransa domin samar da mafita na tsawon lokaci don inganta samar da ruwan sha a jihar.

Gwamnan ya kuma ce gwamnati za ta ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa tsaro a kewayen kayan aikin ruwa.

“Kuma duk wanda aka samu yana so zai fuskanci fushin shari’a. Muna yin dabarun kan hakan da gaske.

“Gwamnati tana tsara hanyoyin samar da na’urorin ruwa masu nauyi, injina masu ƙarfin wuta, sarrafa satar waya da sauransu.

“Muna tabbatar wa mutanenmu cewa abin da muke da shi a kan tebur, shi ne na gajeren lokaci, tsakiyar wa’adi da kuma dogon lokaci,” in ji shi.