An yi kira ga ‘yan kasuwa su kasance masu jinƙan mabuƙata

Daga DAUDA USMAN a Legas

Shugaban kasuwar ƙasa da ƙasa ta mile12 da ke birnin Legas, Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam (Dallatun Egbaland) ya yi kira ga ‘yan kasuwa da masu hannu da shuni da su kasance masu taimakon mabuƙata da gajiyayyu a cikin wannan wata na Ramadan.

Samfam ya kuma shawarcin ‘yan kasuwar Mile12 su kasance masu yawaita ziyarar ‘yan uwa da abokan arziki domin samun lada mai tarin yawa.

Shugaban kasuwar, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da ziyarar sa a waɗansu ɓangarorin kasuwar tare da shawartar waɗansu masu kuɗi daga cikin su da su cigaba da tallafa wa marasa ƙarfi a cikin wannan wata mai alfarma tare da ciyar da gajiyayyu.

Ya ce ya zama wajibi ga al’ummar Musulmin duniya da su cigaba da bin umarni tare da bin dokokin addinin Musulunci, inda kuma ya shawarci ‘yan kasuwa musamman masu sayar da kayayakin da ake yin sahur da su da buɗe baki da su ƙara ƙoƙari wajen tausaya wa al’ummar Musulmi a cikin wannan watan na Ramadan.