Jonathan ya tsallake rijiya da baya a haɗarin mota

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya tsallake rijiya da baya a wani haɗarin mota, wanda ya kai ga rasa muƙarrabansa na tsaro su biyu. Lamarin ya faru ne ranar Larabar nan da ta gabata.

Har yanzu babu cikakken bayani kan lamarin, amma kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka ruwaito, haɗarin ya afku ne a lokacin da tsohon shugaban ke kan hanyarsa ta zuwa gidansa da ke Abuja daga filin jirgin sama.

Mai taimaka wa Jonathan kan harkokin yaɗa labarai ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwa.

Da yake tsokaci kan lamarin, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ce, “wannan labari ya girgiza mu. Muna godiya ga Allah da ya tseratar da rayuwar shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan. Amma abin takaici ne yadda ya rasa mataimakansa biyu a haɗarin mota.

“Ina ta’aziyya ga iyalan marigayin da kuma Shugaba Jonathan. Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu ya huta lafiya,” inji Atiku.