Kotu ta tabbatar da tuhuma bakwai kan Nnamdi Kanu

Daga BASHIR ISAH

Alƙali Binta Nyako ta Babbar Kotun Abuja, ta yi watsi da laifuffuka 8 daga cikin laifuffuka 15 da Gwamnatin Tarayya take tuhumar jagoran masu rajin kafa ƙasar Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu.

A ranar Juma’a Alƙali Binta ta kuɓutar da Nnamdi Kanu daga tuhumar aikata laifuffuka takwas ɗin bayan da ta nazarci bayanan da Kanu ya gabatar wa kotun yana mai ƙalubalantar tuhume-tuhumen da Gwamnatin Tarayya ta yi masa.

Alƙalin ta ce, ta karanta bayanan da Kanu ya gabatar da kyau kuma ba ta ga wani laifi ba a tuhuma ta 6, 7, 8, 9, 10, 11, 12 da 14 da aka yi wa wanda ke kare kansa.

Ta ƙara da cewa, “Tuhuma ta 1, 2, 3, 4, 5, 8 da ta 15 na da ɓurɓushin zargin da Kanu zai bada amsarsu.”

Tana mai cewa, “Kotu za ta ci gaba da yi wa Kanu shari’a a kan waɗannan tuhume-tuhumen.”