Caji ba bisa ƙa’ida ba: fiye da masu ajiya 2000 sun koka da bankuna

Daga AMINA YUSUF ALI

Fiye da masu ajiya 2,256 ne suka shigar da koken su zuwa ga ƙungiyar Ma’aikatan bankuna(CIBN), game da yadda bankuna suke cirar musu kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba. Kuɗaɗen da ake zargin an cirar wa kwastomomi masu ƙorafin sun kama har Naira biliyan 368.9 da Dala miliyan $428.7 wato dai-dai da Naira 177.05.

Waɗannan bayanai suna ƙunshe a cikin rahoton shekarar 2021 da ƙungiyar ta  saki a ranar Asabar ɗin da ta gabata, jim kaɗan bayan kammala babban taronta na shekara-shekara a jihar Legas. 

Shugaban ƙungiyar ta CIBN, Dakta. Bayo Olugbemi shi ne ya jagoranci taron wanda ya samu halartar mambobin ƙungiyar da suka zo daga ɓangarori da dama na ƙasar nan.

Kodayake, ƙungiyar ma’aikatan bankin sun bayyana cewa, a halin yanzu sun samu nasarar warware kesa-kesai  2,206 daga cikin koken da aka kawo musu. 

Hakazalika, sun bayyana cewa an kashe Naira biliyan 30.65bn da Dala $19.48 a kan warware ƙorafe-korafen.

A ƙarshen taron ne aka gudanar da zaɓen sabbin shugabannnin ƙungiyar ma’aikatan bankin (CIBN). Yayin da ake sa ran  shugabanta mai ci na yanzu, Dakta Bayo Olugbemi zai miƙa ragamar shugabancin ƙungiyar ga sabon zaɓaɓɓen shugabanta, Dakta Kenneth Opara a ranar 21 ga watan Mayun shekara ta 2022. Wato zai gaji gadon Dakta Olugbemi wanda ya shafe shekaru biyu a gadon mulkin. 

Shi dai Dakta Opara shi ne shugaba na 22 da ƙungiyar za ta yi. Sannan kuma ƙungiyar ta zaɓi sabbin jami’ai sannan kuma yi bitar rahotonta na shekara a kan kuɗi da sauran al’amura.