A wata uku ‘yan bindiga sun kashe mutum 3,000 a Nijeriya – Bincike

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wani rahoton binciken da aka gudanar a Nijeriya ya ce mutane 2,968 ‘yan bindiga suka kashe a jihohin Neja da Kaduna da Zamfara a cikin watanni 3, yayin da aka yi garkuwa da wasu 1,484.

Binciken da ƙungiyar sanya ido akan harkokin tsaron Nijeriya ta gudanar da ake kira ‘Nigeria Security Tracker’ ya ce mutanen da ake kashewa a yankin Arewa maso Yamma ya zarce wanda ake yi a kowanne sashe.

Rahotan binciken ya ce ‘yankin Arewa ta tsakiya ita ce ta biyu wajen kashe-kashen, inda ta yi asarar mutane 984, sai kuma Arewa maso Gabas wacce ta yi asarar mutane 488.

A yankin Kudu maso Gabas inda ake fama da masu fafutukar kafa ƙasar Biafra, an hallaka mutane 181 a waɗannan watanni, yayin da aka kashe mutane 127 a Kudu maso Yamma da 85 a Kudu maso Kudu.

‘Yan bindigar da aka bayyana a matsayin ‘yan ta’adda na ci gaba da kai munanan hare-hare yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya inda suke hallaka mutane tun daga shekarar 2017.

Waɗannan mahara sun kashe mazauna karkara da kwashe dukiyoyin su da kuma garkuwa da wasu daga cikin su domin karɓar fansa, yayin da manoma da matafiya ma basu tsira ba daga hare-haren waɗannan mutane.

Yayin da ‘yan bindigar ke hallaka jama’a a Arewa maso Yamma, mayaƙan Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabas.