Sabbin shugabannin APC za su yi taronsu na farko a Afrilu

Daga BASHIR ISAH

Kwamitin Shugabanni na Ƙasa na jam’iyyar APC, ya tsayar da ranar 20 ga Afrilu a matsayin ranar da zai yi taro don tsara jadawali da kuma shiryen-shiryen fid da gwani na zaɓen 2023.

Sakataren yaɗa bayanai na jam’iyyar na ƙasa, Mr Felix Morka ne ya sanar da hakan ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce taron zai gudana ne a zauren taro na otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja, tare da cewa a wajen taron ne jam’iyyar za ta yi nazarin ‘yan takaran da za su tsaya zaɓe a 2023 ƙarƙashin APC.

Morka ya ce, “La’akari da Doka ta 25.2.ii na kundin tsarin mulkin APC, Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) ya yi kira da ashirya taro na farko bayan babban taron jam’iyya ƙarƙashin Kwamitin Shugabanni (NEC) wanda zai gudana ranar Laraba, 20 ga Afrilun 2022.

“Da wannan, an buƙaci ɗaukacin mambobin NEC da su halarci wannan taro kamar yadda Doka ta 12.3 ta tanadar a cikin kundin tsarin mulkin APC.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *