Kare ’yan Nijeriya daga ’yan ta’adda

Duk da cewa batun tsaro shi ne babban abin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta sa a gaba, amma ’yan Najeriya masu bin doka da oda a yanzu suna rayuwa cikin fargaba fiye da kowane lokaci a tarihin ƙasar.

Mutanenmu sun dogara sosai kan tafiye-tafiye don samun abin rayuwa, amma abubuwan da suka faru a cikin makonnin da suka gabata sun nuna cewa tafiye-tafiyen ya zama wani abu mai hatsarin gaske a halin yanzu.

Ta’addancin ’yan bindiga na neman zarce na ƙungiyar Boko Haram/ISWAP a matsayin babban hatsarin da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin ’yan Nijeriya. A cikin makonnin da suka gabata kaɗai ’yan ta’adda sun kai hari filin jirgin saman Kaduna tare da kashe wani mai gadi.

KARANTA: Watan Ramadana mai albarka

Kamfanonin jiragen sama guda biyu na Air Peace da Azman Air sun tsallake rijiya da baya daga harin bayan da suka tashi sa’o’i kaɗan kafin ’yan ta’addar da ke kan babura su iso.

Har yanzu dai ana zubar da jini a Nijeriya sakamakon harin da ’yan ta’addan, inda a makonnin baya suka kai hari kan wani jirgin ƙasa da ya taso daga Abuja kan hanyar Kaduna. Mutane 8 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, sannan ba a san adadin mutanen da suka ɓata ba.

Wasu jerin bidiyoyi da manema labarai suka samu a kwanakin baya na farmakin da ’yan ta’addan suka kai wa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna na ranar 28 ga watan Maris ya bayyana miyagun ɗauke da muggan makamai a cikin ƙungurmin daji zagaye da waɗanda suka sace inda jama’ar ke roƙon gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa.

‘Yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna sun saki sabon bidiyon fasinjojin da suka yi garkuwa da su.

A bidiyon, an ga ɗaya daga cikin fasinjojin na bayyana cewa akwai iyaye mata, yara, tsoffi, marasa lafiya da kuma jigatattu a cikinsu, don haka gwamnati ta cika sharuɗɗa.

Duk da haka, har yanzu ba a san sharuɗɗan da ‘yan ta’addan suka gindaya wa gwamnati ba, a bayyane ya ke cewa mambobin ƙungiyar ta’addanci ne suka kai farmakin. 

Kamar dai hakan bai wadatar ba, jaridar Blueprint a ranar Juma’a 1 ga Afrilu, 2022 ta ruwaito ta’addanci da masu garkuwa da mutane a Abuja da kuma jihohin Benue, Kaduna, Ribas da Ogun suka yi, inda aka yi garkuwa da mutane 15. An yi garkuwa da huɗu daga cikinsu a unguwar Bukpe da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar da sojoji kuma suka daƙile wani harin ta’addancin da aka kai garin Gurara da ke kusa da Abuja. Yawancin waɗanda aka sace matafiya ne.

Babu inda ke da zaman lafiya yanzu a Nijeriya. A yayin da ’yan ta’adda da ’yan bindiga ke safarar matafiya tare da yin garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, a hankali a hankali al’ummar ƙasar na samun tangarɗa sakamakon gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.

Haka kuma jerin hare-haren da aka kai a filin jirgin na Kaduna ya nuna cewa hatta zirga-zirgar jiragen sama bai zama wurin tsaro ba ga manyan mutane. ’Yan ta’addan da suka harbo wani jirgin soji na iya kai hari cikin sauƙi idan har Gwamnatin Tarayya ba ta farga da nauyin da ke kanta ba.

Yanzu dai ’yan Nijeriya ba su yi mamakin yadda shugabannin ’yan sanda da na soji da na sauran jami’an tsaro ke cigaba da zama a kan muƙamansu ba, sakamakon gazawarsu wajen gudanar da ayyukansu. Kimanin shekaru shida ’yan Nijeriya suka yi ta ihu da kakkausar murya suna kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya sake naɗa manyan hafsoshin tsaro, wanda komai ya dawo baya yanzu.

A makon da ya gabata ne dai zaɓaɓɓun jami’an jam’iyyar APC mai mulki, suka fito fili suka bayyana wa ’yan Nijeriya gazawar gwamnatinsu wajen kare ’yan Nijeriya. Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Dakta Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, ya nemi afuwar wannan gazawar. Haka kuma, ’yan jam’iyya mai mulki a majalisar wakilai, sun fito ƙarara sun yi kuka tare da bayyana irin yadda gwamnatinsu ta yi wa ’yan Nijeriya.

Dole ne mu wuce matakin kuka. Mutanen da suka kasa yin ayyukansu dole ne su fuskanci sakamako kamar yadda dokokinmu na Kundin Tsarin Mulki suka tsara. Kukan jama’a ko ƙorafin gazawa ba zai taimake mu ba.
Yakamata gwamnonin ta ɗauki lamarin tare da haɗin gwiwar al’ummar yankinsu. Ta hanyar haɗin gwiwar ’yan ƙasa, za mu iya kwato dazukanmu da wuraren gwamnati daga hannun ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.