Elon Musk ya sama wa Tiwita ribar shekara huɗu cikin kwana ɗaya da sayen hannun jarinsa

Daga AMIN YUSUF ALI

Mutumin da ya fi kowa arziki a Duniya, Biloniya Elon Musk ya ƙara samar da riba mai yawa ga kamfanin Tiwita jim kaɗan bayan sayen hannun jari a kamfanin na  Tiwita.

Attajiri Elon Musk ya samar da gwaggwaɓar riba har ta dalar Amurka guda Kwatankwacin Naira Biliyan 580 bayan awanni ashirin da huɗu da sayen hannun jarin Kamfanin Tiwita na kaso 9.2%.

A cewar ƙididdigar Jaridar Ingilishi ta kasuwanci, Bloomberg Mutumin da ya fi kowa arziki ya samu ribar dalar Amurka guda bayan samun shiga da zama ɗaya daga cikin mamallakan Kamfanin nan na sada zumunta na Tiwita.

Jaridar ta kuma rawaito cewa, Musk wanda shi ne shugaban kamfanin ƙera motoci na Tesla ya sayi hannun jarin Tiwita ɗin ne a kan Dalar Amurka biliyan 2.9, inda ga shi ya kusa mayar da kuɗinsa a cikin awanni 24 kacal.

A cewar majiyarmu, wannan riba da ya samu, ita ce kafatanin ribar da kamfanin Tiwita ya samu daga shekaru huɗu baya zuwa yau. Wato dai gwari-gwari, Elon Musk ya samar wa kamfanin ribar shekaru huɗu a cikin awanni 24 kacal. 

Elon Musk wanda da ma babban mai sukar kamfanin Tiwita ne, a daren ranar da abin ya faru ya wallafa wani rubutu ne wanda ya jawo ra’ayin miliyoyin masu amfani da shafin. A rubutun nasa ya nemi jin ra’ayoyin mutanen Duniya masu amfani da Shafin Tiwita a kan ko a sanya maɓallin da zai ba da damar tace rubutu ko a’a. 

Wannan rubutun ya jawo cece-kuce kuma ya yamutsa hazo sosai a shafin. An tafka muhawara sosai a kan ra’ayin.

Daga ƙarshe dai an tattara adadin yawan mutanen da suka bayyana ra’ayoyinsu sun kai 2,382,075, inda kaso 73.6 suke goyon bayan a samar da maɓallin tace rubutun. Wannan shi ne dalilin da ya jawo masa samun gwaggwaɓar ribar. 

Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban kamfanin Tiwita, Parag Agrawal, ya nemi Elon Musk da ya zo ya amshi muqaminsa a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin gudanarwa na Kamfanin.