Ƙasar Sin na adawa da amfani da batutuwan da suka shafi haƙƙin ɗan Adam wajen matsawa wasu ƙasashe lamba

Daga CMG HAUSA

Dangane da matakin da babban taron MDD ya ɗauka, na dakatar da Rasha daga zama mamba a kwamitin kare haƙƙin bil Adama na MDD, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya jaddada matsayin ƙasarsa a taron manema labarai da aka saba gudanarwa a Jumma’ar da ta gabata, inda ya jaddada cewa, ƙasar Sin tana adawa da siyasantar da batutuwan da suka shafi haƙƙin ɗan Adam, da nuna adawa da yin zaɓe, da nuna kiyayya, kuma bisa amfani da ma’auni biyu kan batutuwan, kana da adawa da amfani da batutuwan haƙƙin dan Adam wajen matsa lamba ga sauran ƙasashe.

Yayin da yake amsa tambayar, Zhao ya yi nuni da cewa, “Ba a bayyana yadda aka tsara ƙudurin a fili ba, kuma ba a yi shawarwari da dukkan ƙasashe mambobin kwamitin kamar yadda aka saba, don sauraren ra’ayinsu sosai ba.

Irin wannan matakin zai kara faɗaɗa rarrabuwar kawuna a tsakanin ƙasashe mambobin, ta yadda za su kara samun sabani a tsakanin ɓangarori masu ruwa da tsaki, kana za a ƙara hura wutar rikici, kuma hakan ba zai yi amfani wajen kawar da rikici, balle ma taimakawa wajen inganta shawarwarin zaman lafiya ba.

Mai fassara: Bilkisu