Buhari bai tafi London ba – Bashir Ahmad

Daga BASHIR ISAH

An labarin da ke nuni da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi hutun kwana 20 a London, hakan ba gaskiya ba ne.

A yau ne dai aka ga wani rahoto kan tafiyar Buhari zuwa hutun kwana ashirin a London ya karaɗe kafafen sadarwa.

Sai dai a cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai taimaka wa Shugaba Buhari kan sha’anin kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad ya ƙaryata labarin.

Yana mai cewa, lallai Shugaba Buhari yana Abuja bai tafi ko’ina ba, kuma babu wani shiri a kan zai tafi London.