Rashin wutar lantarki ya hana jiragen sama tashi a Legas

Daga WAKILINMU

Sakamakon matsalar ɗaukewar wutar lantarki da aka fuskanta a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Lagas, hakan ya jaifar da cikas wajen tashin jirage a filin, kana aka bar tarin fasinjoji zaune cikin zullumi na wani ɗan lokaci.

Bayanai sun nuna ɗaukewar wutar wanda ya faru a safiyar Asabar da ta gabata, ya hana jiragen sama tantance fasinjojinsu, lamarin da ya haddasa cunkoso a filin jirgin.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wutar lantarkin ta ɗauke ne sakamakon ruwan sama mai karfi da aka samu a ranar Juma’a da daddare zuwa wayewan garin Asabar.

Wannan al’amari ya shafi jirage da dama kasancewar ya auku ne a daidai lokacin da yawancin jiragen waje ke sauka da tashi.

Manajar filin jirgin saman, Victoria Shin-Aba, ta ce ɗaya daga cikin hanyoyin samun wutar nasu ne ta samu matsala sakamakon ruwan saman da aka yi.

Tuni dai Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da bada haƙuri kamar yadda yake ƙunshe cikin wata sanarwar da ta fitar.