Kwastom ta cafke motar ‘yan sanda da ake shigo da shinkafa da ita

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar hana fasa-ƙwauri (Kwastom) dake kula da shiyar jihar Ogun ta kama motar ‘yan sanda maƙare da shinkafar gwamnati.

Shugaban hukumar Kwastom Shiyyar Jihar Ogun, Bamidele Makinde ya sanar da haka ranar Talata da ta gabata yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Abeokuta.

Makinde ya ce, motar da hukumar ta kama ƙirar ‘Hilux van’ na xauke da lambar PF 10889 SPY sannan an loda ta da manyan buhunan shinkafa 2,750. Ya ce direban dake tuka motan dai ya gudu.

Makinde ya ce, duk da an ga motar da lambar motar ‘yan sanda da jiniya, ba a tabbatar ba ko kayan na ‘yansandan ba ne har yanzu tukunna.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ya ce ba shi da masaniya akan kamen da hukumar Kwastom ta yi amma ya ce zai gana da manema labarai da zarar ya samu bayanai a kai.

Bayan haka, Makinde ya ƙara da cewa, hukumar ta kama buhunan shinkafar gwamnati 5,429 daga 9 ga Fabrairu zuwa 21 ga Maris.

Ya ce a tsakanin wannan lokaci hukumar ta kama buhuna 133 da ƙulli 181 na tabar wiwi, motoci 18, jarkokin man gyaɗa 13, buhuna biyu da dilolin gwanjo.

Hukumar ta Kuma kama buhuna 25 da dilolin takalma na gwanjo, kwalaye 880 na naman kaji da lita 26,725 na man fetur.