Ali Nuhu ya zama jakadan wani kamfani a Arewacin Najeriya

Daga AMINA YUSUF ALI
 
An naɗa fitaccen jarumin finafinan Hausa na Kannywood, Ali Nuhu, a matsayin jakadan kamfanin Checkers Custard na Arewacin Najeriya.

Jaridar yanar gizo ta Labarai24.com ta rawaito cewa, an yi naɗin ne a wani taro da kamfanin Checkers Africa suka shirya a jihar Kano da ke Arewa maso yammacin ƙasar.

A cewar babban Manajan Kamfanin Checkers da ke nahiyar Afirka, Mista Karan Checker ya bayyana cewa, la’akari da irin shaharar da jarumin ya yi a masana’antar Kanywood da arewacin Najeriya ya sanya kamfanin na Checker ya naɗa shi a matsayin jakadansu na shiyyar Arewa.

A yayin  da ya ke jawabinsa, Mista Karan Checker, ya bayyana cewa, kamfanin ya kuma yi la’akari da cewa Kano ce cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya, kuma miliyoyin al’ummar arewa na amfani da kayayyakin kamfanin sosai.

Haka kuma Mista Karan, ya ce kayayyakin kamfaninsu da suka haɗa da Checkers Custard na kan gaba wajen aminci da nagarta, wanda hakan ne ya sanya suke jerawa da sauran kayayyakin kamfanonin duniya.

Ya ƙara da cewa, Checkers Custard ta bambanta da sauran musamman wajen ɗanɗano da kuma sinadaran da kan ƙara lafiyar jiki da kuma sanya kuzari ga wanda ya yi amfani da ita.

Lokacin da Jarumi Ali Nuhu ke karvar shaidar zama jakadan Checkers Custard, ya bayyana jin daɗinsa game da wannan naɗin da aka yi masa tare da yin godiya ga hukumomin kamfanin na Checkers.

Jarumi Ali Nuhu ƙara da cewa, ba wai kawai yana murna da wani abu da zai samu daga wannan naɗi ba, sai dai yadda burinsa ya cika a matsayinsa na mai amfani da Checkers Custard.

Jarumin ya ce wani abin sha’awa da Checkers Custard shi ne yadda aka yi ta daidai da farashin da kowa zai iya saya. Kuma sinadaran da ke cikinta zai yi amfani ga mace da namiji da yaro da kuma babba, kuma mutum zai iya amfani da ita kowanne lokaci.

A ƙarshe, Ali Nuhu, ya yi kira ga al’ummar Arewa da ma Najeriya baki ɗaya akan su cigaba da amfani da kayayyakin kamfanin Checkers musamman garin Custard na kamfanin.