Sin na fatan Amurka da NATO za su koma shawarwari tare da Rasha

Daga CMG HAUSA

Ƙasar Sin ta yi kira ga Amurka da ƙungiyar tsaro ta NATO, da su hau teburin shawara tare da ƙasar Rasha, ko a kai ga warware ricikin Ukraine yadda ya kamata.

Da yake bayyana hakan, yayin taron manema labarai na yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi watsi da zargin da wasu ƙasashe ke yi wa Sin, yana mai cewa, har kullum Sin na kan manufar riko da gaskiya da adalci ne game da batun Ukraine.

A jiya Alhamis 24 ga wata, kakakin tawagar Sin a ƙungiyar EU, ya ce sanarwar bayan taron NATO, ta zargi Sin ba tare da wani dalili ba, tare da ɗorawa ƙasar karan tsana da nufin muzgunawa, matakin da ko alama Sin din ba za ta amince da shi ba.

Jami’in ya ce, ya zama wajibi ƙasar Sin ta tunatar da NATO muhimmancin fahimtar matsayar Sin, domin kuma a ko da yaushe, Sin din na martaba ikon ƙasashe na mulkin kai, da ‘yanci da tsaron yankunan dukkanin ƙasashe, bisa ka’idar martaba dokokin MDD.

Ya ce tun bayan ɓarkewar rikicin Ukraine, bisa rungumar gaskiya da adalci, Sin ta yi aiki tukuru, wajen yayata tattaunawar wanzar da zaman lafiya, da dakatar da buɗe wuta, da kiyaye aukuwar mummunan yanayin jin kai a ƙasar.

Fassarawa: Saminu