Gwamnatin Jigawa ta gudanar da rigakafin cutar dabbobi

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Gwamnatin Jihar Jigawa ta gabatar da rigakafin cutar dabbobi a Ƙaramar Hukumar Kaugama da ke jihar.

A jawabin da ya gabatar a lokacin ƙaddamar da allurar rigakafin, shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Idris Mati Hadi ya jaddada ƙudurin sa na tallafa wa makiyaya domin inganta lafiyar dabbobin su.

Ya kuma yi kira ga makiyaya da su kai dabbobin su cibiyoyin rigakafi mafi kusa da su domin cin gajiyar shirin.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban sashin aikin gona da albarkar ƙasa na yankin, Alhaji Ado Musa ya ce kimanin dabbobi dubu 35 da suka haɗar da shanu da tukamaki da awaki da kuma karnuka ake sa ran yi wa rigakafin.

Ya ce ƙaramar hukumar ta ɗauki ma’aikatan wucin-gadi guda 15 domin gudanar da aikin a mazaɓun yankin guda 11.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *