’Yan jarida sun karrama gidan kangararru da gyaran hali a Jihar Bauchi

Daga ABUBAKAR A. BOLARI

Wata ƙungiyar ‘yan jarida mai suna ROJOF (Rehabilitations and Orphanage Journalist Covering Forum Bauchi) da suke bayyana aikace-aikacen wani gidan gyaran hali da tarbiyyar kangararru a jaridu da kafafaen yaɗa labarai a jihar Bauchi mai suna ‘Malam Kawu Youth Rehabilitation and Orphanage Centre’ sun karrama gidan sakamakon gamsuwa da yadda yake gyara tarbiyyar matasan.

Ƙungiyar ta karrama mamallakin gidan ne mai suna Dakta Abdullahi Muhammad Tahir da ake kira Malam Kawu, saboda yadda jama’a suka gamsu da yadda yake kula da kangararrun ‘ya’yan su da suka samu matsalar ƙwaƙwalwa sakamakon shaye-shaye da sauran su.

A jawabin shugaban ƙungiyar ta ROJOF, Usman Abbas Shehu Gungura, Uskuleto, cewa ya yi sun duba irin gudunmawar da Dakta Abdullahi Muhammad Tahir, yake bayarwa ne a cikin al’umma ya sa suka karrama shi da lambar yabo  domin yin hakan wata dama ce da zai sa gwamnati ko ƙungiyoyi masu zaman kansu su shigo don tallafawa.

Abbas Usman Gungura, ya ƙara da cewa yanzu haka a wannan gida na gyaran hali na Malam Kawu Youth Rehabilitation and Orphanage Centre dake Ƙofar Turwun akan Titin Yakubu Wanka a cikin garin Bauchi yana da matasa kimanin 100 da ake wa gyaran hali, sannan akwai almajirai guda 700 da ba sa fita don yin bara, kuma cin su da shan su da suturar su duka shi yake musu kyauta.

A cewar sa, a ciki ana kawo matasa ne daga ko’ina a ƙasar nan, amma a halin yanzu haka akwai kimanin matasa guda 100 da suka samu taɓuwar ƙwaƙwalwa saboda matsalar shaye-shaye da ake gyara musu tunani kuma kowa yana ganin ci gaban da wannan bawan Allah Malam Kawu yake samarwa.

Har ila yau akwai yara guda 50 da suke makarantar firamare, guda 30 kuma suna makarantar sakandare, sannan mutum 10 da suke manyan makarantu, kama daga ATBU da ‘Polytechnic’ dukkan su kuma a aljihun sa ne yake biya musu kuɗaɗen makaranta, sannan ana koya musu sana’a.

A nasa tsokacin, shugaban gidan gyaran halin na Malam Kawu Youth Rehabilitation and Orphanage centre, Dakta Abdullahi Muhammad Tahir, cewa ya yi wannan cibiya ta gyaran hali da kula da kangararru tana aiki ne kafaɗa da kafaɗa da hukumar nan ta hana sha da  fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma gidan gyaran hali wato gidan fursuna wajen gudanar da aikace-aikacen su.

Dakta Abdullahi Muhammad Tahir, ya kuma ce yaran da ake kawo masa ‘ya’yan manyan attajirai ne da ‘yan siyasa da suke Bauchi, kuma da za a bar su a gari da sai sun fitini kowa.

Ya ƙalubalenci gwamnati na rashin kulawa da irin waɗannan gidajen gyara hali da kula da marayu  amma sukan iya kashe kuɗaɗe masu yawa wajen gine-ginen ɗakunan kwanan ɗalibai a makarantun gwamnati.

Shi ma Farfesa Bala Sulaiman, daga Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa dake Bauchi, ya jawo hankalin gwamnati da cewa inganta irin waɗannan gidaje ya fi gina jami’o’i  barkatai da ba su da amfani a ƙasar nan, saboda kullum ana cikin yajin aiki, inda ya ce domin idan waɗannan kangararru za su kasance a cikin al’umma ba za a samu zaman lafiya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *