Ba ma’aikacinmu da ya rasa ransa a gobarar kamfanin simintin BUA a Sakkwato – BUA

Daga AMINA YUSUF ALI

Kamfanin Samar da Siminti na BUA dake Sakkwato ya bayyana cewa, mutum uku da suka mutu a sanadiyar gobarar da ta tashi a masana’antar Simintin BUA a Sakkwato, ba ma’aikatan kamfanin ba ne, ‘yan ina-da-aiki ne.

Wannan bayani yana ƙunshe ne a wata sanarwa da Sada Sulaiman, Daraktan Gudanarwa na BUA Cement ya aiko wa Jaridar PREMIUM TIMES.

Ya qara da cewa,  waɗanda tsautsayin ya ritsa da su, suna aiki ne a ƙarƙashin wani mai aikin kula da gyare-gyare na lafiyar inji.

A kwanakin baya da ma jaridar ta buga labarin yadda wuta ta tashi a masana’antar Siminti ta BUA a ranar Juma’ar makon  mutum uku suka mutu, kuma wasu da dama suka samu raunuka.

Sada Sulaiman ya bayyana cewa, wutar ta tashi a ɗakin da ake ajiye baƙin mai, kuma an yi ƙoƙari sosai an kashe wutar kafin ta kai ga shafar wasu ɓangarori na masana’antar.

“Lokacin da gobarar ta tashi an yi sauri an kira jami’an kashe gobara, su da ɓangaren kashe gobara na BUA, sun yi matuƙar ƙoƙari sun kashe wutar, sun kuma hana ta lasar wani ɓangare.

“Waɓanda suka mutu ba ma’aikatan BUA ba ne, ‘yan ina-da-aiki ne da suka zo aikin gyara tare da wani mai yi wa kamfanin gyare-gyare.

“Har yanzu ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba. Amma jami’an Kashe Gobara da namu na kamfani su na ƙoƙarin binciko musabbabin tashin gobarar.
“Muna miƙa ta’aziyyar waɗanda suka mutu, kuma muna yin jaje ga waɗanda suka ji ciwo.” Inji shi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *