Ci gaban da ke mayar sa hankali kan jama’a na da muhimmanci ga kare haƙƙoƙinsu

Daga CMG HAUSA

Zaunannen jakadan ƙasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, Chen Xu, ya ce ci gaban dake mayar da hankali kan jama’a, shi ne ya kamata ya kasance jigon dabarun kawar da rashin daidaito a tsakanin al’ummun duniya.

Chen Xu, wanda ya bayyana haka ga taro na 49 na hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta MDD a Geneva, ya ce annobar COVID-19 ta yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin duniya da ci gaban rayuwar jama’a, musammam ma rayuwar jama’ar ƙasashe masu tasowa.

Wannan ya ta’azzara rashin daidaito da haifar da ƙalubaloli masu tsanani ga ci gaban duniya. Don haka, ya kamata ƙasashe su mayar da hankali wajen inganta ci gaban dake mayar da hankali kan jama’a, musammam magance rashin daidaito ta fannin ci gaba a tsakanin ƙasashe, ta yadda ba za a bar kowa a baya ba.

Ya ƙara da cewa, jigon demokuraɗiyyar ƙasa ya dogara ne da ko al’ummarta ne ke kan gaba a dukkan manufofinta, haka kuma ko tana warware matsalolin da suke fuskanta ko a’a.

Jakadan na ƙasar Sin ya bayyana cewa, yayatawa da kare demokuraɗiyya da haƙƙoƙin jama’a, haƙƙi ne na bai daya da ya rataya kan ƙasa da ƙasa. Kana bai kamata ya zama wata hanya ta matsawa ƙasashe lamba ba.

Bugu da ƙari, ya ce duk wata ƙasa dake keta ƙa’idojin demokuraɗiyya da yin katsalandan cikin harkokin cikin gida na ƙasashe masu cikakken ‘yanci, bisa fakewa da kare demokuraɗiyya da haƙƙoƙin jama’a, wadda kuma ke yunƙurin ƙaƙaba nata tsarin demokuraɗiyya kan wasu, to ta yi hannun riga da ainihin ma’anar demokuraɗiyya.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha